Wataƙila Jorginho ya koma taka leda a kakar bana bayan jinyar huhu

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce ɗanwasansa na tsakiya Jorginho yana "samun sauƙi" daga jinyar huhu, inda ya ce da alama ɗanwasan zai iya komawa taka leda a kakar bana.
Wasan ƙarshe da ɗanwasan mai shekara 33 ya taka shi ne a 12 ga Afrilu, amma aka cire shi a ƙarshen wasan, wanda ƙungiyar ta yi kunnen-doki da Brentford saboda zafi da yake ji a ƙirginsa.
Da yake jawabi a game da wasan ƙungiyar na Premier na ranar Asabar da za su fafata da Bournemouth, Arteta ya ce: "Yana samun sauƙi."
Arsenal ba ta tabbatar da irin jinyar da yake yi ba, amma wata majiya ta ce ya ji ciwo ne a huhunsa.
A game da yiwuwar mataimakin kyaftin ya taka wasa a kakar bana, Arteta ya ce: "ina tunanin idan komai ya fi daidai, zai dawo taka leda a wasu makonni a nan gaba."
Jorginho na gab da ƙarshen kwantiraginsa a Arsenal, inda ake tunanin zai bar ƙungiyar kafin kakar baɗi.
Ɗanwasan ɗan asalin ƙasar Italiya ya buga wasa 78 tun zuwansa ƙungiyar daga Chelsea a Janairun 2023 a kan fam miliyan 12.
Shi ma Kai Havertz akwai alamar zai koma taka leda a kakar bana bayan jinyar da yake yi.












