Arsenal na neman Sane, Barcelona ta yi watsi da tayin United kan de Jong

 Leroy Sane

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal na sha'awar ɗaukar ɗan wasan Jamus Leroy Sane a kyauta idan kwantiragin ɗan wasan mai shekaru 29 da Bayern Munich ya ƙare a bazara. (Christian Falk)

Barcelona ta yi watsi da tayin fam miliyan 57.8 da Manchester United ta yi na sayen ɗan wasan tsakiya na Netherlands Frenkie de Jong, mai shekara 27. (Fichajes)

Kocin Barcelona Hansi Flick na son ci gaba da riƙe De Jong ko ta halin ƙaƙa, kuma kulob ɗin na Catalunya ya sake buɗe tattaunawa kan ƙulla sabuwar yarjejeniya da ɗan wasan. (Sport)

Sabon daraktan ƙwallon ƙafa na Arsenal Andrea Berta na sha'awar ɗaukar ɗan wasan Newcastle ɗan ƙasar Brazil Bruno Guimaraes mai shekaru 27 da kuma ɗan wasan Real Sociedad ɗan ƙasar Sifaniya Martin Zubimendi mai shekaru 26. (AS)

Barcelona ma na ta sanya ɗan wasan tsakiya na Newcastle Guimaraes a cikin jerin ƴan wasan da ta ke son ɗauka a bazara. (Football Espana)

Liverpool tasanya ido kan ɗan wasan baya na Ajax Jorrel Hato, mai shekara 19, wanda ya yi wa ƙasar Netherlands wasa sau biyar. (Mail)

Everton na tunanin zawarcin ɗan wasan tsakiyar Newcastle Sean Longstaff mai shekara 27. (Talksport)

Manchester City da Manchester United da Barcelona da Real Madrid sun shiga jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan Bayer Leverkusen ɗan ƙasar Netherlands Jeremie Frimpong, mai shekara 24. (Teamtalk)

Everton na sa ido kan ɗan wasan Tottenham ɗan ƙasar Isra'ila Manor Solomon, mai shekara 25, wanda ke zaman aro a Leeds. (TeamTalk)

Bayer Leverkusen na da ƙwarin gwiwar cewa ɗan wasan Jamus Florian Wirtz, mai shekara 21, zai tsawaita kwantiraginsa a kulob ɗin, duk da cewa ana alaƙanta ɗan wasan da Bayern Munich da Manchester City. (Bild)