Yadda zamani ya ɗaga darajar sana'a da kasuwancin kilishi a duniya

Asalin hoton, Maryam Gatawa
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja, Najeriya
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Sana'ar kilishi da kasuwancinsa, wata harka ce daɗaɗɗiya mai tarihi a ƙasar Hausa, musamman arewacin Najeriya da wasu ƙasashen Afirka da Hausawa suke rayuwa tun shekaru aru-aru.
Sana'ar, wadda ta kasance sana'a ta dauri, a baya ta fi karɓuwa a tsakanin Hausa, kuma ake mata kallon sana'ar gargajiya.
Sai dai kuma kamar yadda Hausawa suke cewa zamani riga, sana'ar a yanzu haka ta fara tafiya da zamani, inda masu harkar suka fara tafiya da zamani wajen inganta sana'ar da kasuwancinsa.
Yanzu abu ne mai sauƙi ka ga mutum ya bayar da sautun kilishi daga ƙasashen waje, ko kuma wanda ya zo hutu ya saya domin komawa da shi.
Sannan akwai manyan kantunan intanet da suke baje-kalon kilishi a shafukan sada zumunta, suna sayarwa, sannan su tura duk inda mutum yake so - har zuwa ƙasashen waje.
A Najeriya, da zarar an ji mutum zai je unguwar Agadasawa da ke jihar Kano, abin da yake fara zuwa tunanin wanda ya san garin shi ne kilishi, kasancewar garin ya yi suna tun zamanunnuka wajen sana'anta kilishi.
Malam Magaji Yusuf Agadasawa, wani dattijo ne da ya gaji sana'ar daga iyaye da kakanni, kuma yanzu haka yake gadar da ita zuwa ƴaƴa da jikokinsu.
"Na fara sana'ar ce tun ina ƙaramin yaro tun muna koyo a hannun ƙannen iyayenmu har muka dawo hannun iyayen namu," in ji shi, inda ya ƙara da cewa ya kai shekara 40 yana sana'ar.

Asalin hoton, Magaji Agadasawa
Yadda sana'ar ta riƙa sauyawa saboda zamani
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A game yadda suke haɗa kilishin, Malam Magaji ya ce babu wahala, domin a cewarsa, "A taƙaice dai ana haɗa shi ne kawai da kayan yaji sai maggi."
Ya ce duk abin da ake nema na duniya suna samu a sana'ar, domin a cewarsa, ta masa komai.
"Babbar ribarta ita ce dai mutum ya yi muhalli, yaransa suna yin karatu sannan kuma kana zaune cikin sutura da rufin asiri na duk wannan matsi da ake ciki za ka ga cewa kai hankalinka a kwance yake saboda ko yaya ake za ka samu ɗan abin da za ka kare kanka na abinci da ci da sha da sutura," in ji shi.
Sai dai ya ce harkar tana sauyawa da samun ci gaba, inda ya ƙara da cewa abubuwa da dama sun sauya.
Ya ce akwai bambanci da dama a tsakanin yadda suke gudanar da harkar a baya da yanzu.
"Na farko dai lokacin muna yara, iyayenmu suna yin tallar kilishi ne suna zagayawa unguwanni- unguwanni, suna yawo da shi a kan wani abu da ke kiran kata - wani abu ne da ake yi daga ƙwarya."
Ya ce ana haka ne ci gaba ya zo aka koma faranti. "Daga kan faranti har sai ya zamanto ana zama a kasa a unguwanni maimakon yawon talla. Shi ma a katako ake ɗaurawa, daga baya aka koma gilashi. Kuma a da muna ƙunshe shi ne a takarda. Yanzu kuma fakiti ake masa leda, sai a zura a cikin fakiti sannan ka rubuta bayananka saboda ko da wani zai neme ka."
Sai dai ya ce su ƴan gadon, yawancin sun fi ƙarfi wajen sana'anta kilishin, inda ya ce dillalan suna zuwa ne su saya, su je su tallata, sannan su riƙa sayarwa har a ƙasashen waje.
A game da yadda ake samun bambancin ɗanɗano, Malam Magaji Agadasawa ya ce kowane ɓangare ɗanɗanonsa ya sha bamban, sannan ya ƙara da cewa kilishinsu yana kai wata biyu zuwa uku ba tare da ɗanɗanonsa ya canja ba.
Ya ce sana'ar ce ta sa ba a cika samun matasan yankinsu a harkokin dabanci da rikice-rikice ba.
"Hakan ya sa nake kira ga gwamnati su agaza wa masu sana'o'i irin namu na gargajiya yadda zai zama sana'ar nan ba ta mutu ba. Waɗanda suke amfana da sana'ar, kama daga yara zuwa mata a gida, suna da matuƙar yawa. Domin mata a gida ne ake kai musu dakan kayan yaji da sauran kayan haɗi."
Ya ce suna da ƙungiya da suka buɗe domin gudanar da kansu a ƙungiyar, "amma dai kowane mamba na cikin ƙungiyar zaman kansa yake yi yana sana'arsa, amma kanmu a haɗe yake."
Maryam Gatawa: Matashiyar da ke da burin yalwata ƙasashen duniya da abincin Afirka

Asalin hoton, Maryam Gatawa
Maryam Gatawa fitacciyar ƴan kasuwa ce, kuma marubuciya, wadda kamfaninta na GatMeals ya yi fice wajen sayar da kilishi da sauran kayan cimaka.
Maryam ta bayyana wa BBC cewa tana sayar da kilishinta a cikin Najeriya da ma ƙasashen waje, sannan ta ce babban burinta shi ne ta buɗe manyan kantunan kayayyakin abincin Afirka a ƙasashen duniya domin sauƙaƙa nemansu ga mazauna ƙasashen.
"Na sayar da kilishina a ƙasashen duniya da yawa. Kama daga Nijar, Togo, Ghana, Kamaru, har zuwa Dubai, India, Burtaniya da Turkiyya da Saudiyya da wasu jihohin Amurka da sauransu.
Ta ce kasuwancin kilishi sana'ace ta gaske, "musamman yanzu da aka zamanantar da shi tun daga sarrafa shi, gasa shi har zuwa sanya shi a mazubi masu tsafta da kyau da jan hankali. Hakazalika samun lambar sahalewa ta Nafdac na taimakawa wajen haɓaka buƙatuwa da kuma sayan kilishi daga ƙasashen waje maimakon kallon da ake masa a matsayin sana'a keɓantacciya ga Hausawa da kuma wuraren zamansu."
Ta ce kafofin sadarwa na zamani suna taimaka mata, inda a cewarta su ne ƙashin bayan kasuwancinta da take samun kwatomomi a cikin Najeriya da ma daga ƙasashen waje.
Ta ce amfani da zamani ya taimaka wajen inganta sana'ar da ƙara samun karɓuwa a duniya.
"Lokacin da na fara sana'ar na fara yinta ne yadda ake yi a da. Misali zan sarrafa na ƙunshe a takarda sai na jefa a baqar leda. Ana cikin haka sai na ga kasuwa ta buɗe, an fara buƙatar kilishin daga ƙasashen waje, sai na faɗaɗa tunani, na shiga kasuwa na samo mazubi masu kyau, waɗanda ake ganin abin da ke ciki domin ƙara tsafta, sannan na rubuta bayanai irin sunan kamfanina na Gatmeals da adireshi da lambar waya a jiki domin wanda zai nema," in ji Maryam, wadda ta ƙara da cewa ba shakka yin hakan ya qara bunkasa kasuwar nata.
A game da wahalar fara shigar da kilishin zuwa ƙasashen waje, Maryam Gatawa ta ce ta samu shigar wa Amurka ne da yake tana da wata lambar sahalewa wacce ta samu bayan ta yi rajista da hukumar Hazard Analysis and Critical Control Points (HACCP).
"Wasu mu tura ta Fedex duk da cewa akwai tsada ainun, wasu ta aika saƙo wato post office, amman galibin kwastomominmu na saya ne ta hanyar wasu da suka zo Najeriya, za su koma sai su tafi musu da shi. Wasu kuma da kansu suke saka order da sun tashi komawa ƙasar wajen sai su wuce da kayansu."
A game da burin Maryam nan gaba, ta ce tana so ta buɗe manyan kantunan kayayyakin abincin Afirka a ƙasashen duniya, "hakan zai faɗaɗa kasuwancin kilishin da kuma karɓuwarsa a ƙasashen duniya. Kuma zai sauqaqa min aikawa ga ɗaiɗaikun kwastomomi."

Asalin hoton, Maryam Gatawa










