Barca ta koma ta biyu bayan doke Dortmund a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Borussia Dortmund ta yi rashin nasara da ci 3-2 a gida a hannun Barcelona a wasa na shida a Champions League da suka kara ranar Laraba a Signal Iduna Park.
Ƙungiyar Sifaniya ta ci ƙwallayen ta hannun Raphinha da kuma Ferran Torres da ya zura biyu a raga.
Ita kuwa mai masaukin baƙi ta ci biyun ta hannun Guirassy, shi ne ya kara na biyu a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Da wannan sakamkon Barcelona ta koma ta biyu a teburin Champions League da maki 15, sakamakon da ta ci wasa biyar aka doke ta karawa ɗaya.
Ita kuwa Dortmund ta fice daga cikin ƴan takwas ɗin farko da maki 12, wadda ta yi nasara huɗu aka doke ta wasa na biyu.
Wannan shi ne karo na uku da suka fuskanci juna a babbar gasar zakarun Turai, kenan Barcelona ta yi nasara ta biyu, Dotrmund ta ci wasa ɗaya.
Wasan da suka kara a tsakaninsu a Champions League:
Champions League Talara 11 ga watan Disambar 2024
- B Dortmund 2 - 3 Barcelona
Champions League Laraba 27 ga watan Nuwamba 2019
- Barcelona 3 - 1 B Dortmund
Champions League Talata 17 ga watan Satumba 2019
- B Dortmund 0 - 0 Barcelona
Barcelona wadda take ta ɗaya a teburin La Liga za ta karɓi bakuncin Leganes ranar Lahadi, sannan Atletico Madrid ta ziyarce ta ranar Asabar 21 ga watan Disamba.
Ita kuwa Dortmund, wadda take ta shida a teburin Bundesliga, za ta kara a gida da Hoffenheim ranar Lahadi, sannan ta je Wolsfburg ranar Lahadi 22 ga watan Disamba a Bundesliga.
Jerin ƴan wasan Barcelona da aka je da su Jamus:
Cubarsí, Balde, R. Araujo, I. Martinez, Gavi, Ferran, Pedri, Lewandowski, Raphinha, Iñaki Peña, Pablo Torre.
Sauran sun haɗa da Fermín, M. Casadó, Pau Víctor, Lamine Yamal, Olmo, F. De Jong, Kounde, Eric, Szczęsny, Astralaga, H. Fort da kuma Gerard Martín.
Sakamakon wasannin Champions League na ranar Laraba:

Asalin hoton, BBC Sport











