Real Madrid ta cire rai kan Alphonso Davies, United na zawarcin Vlahovic

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta fara cire rai kan ɗaukar ɗan wasan baya na Bayern Munich Alphonso Davies, mai shekara 24. (Goal)
Manchester United ta ƙara sunan ɗan wasan Serbia da Juventus Dusan Vlahovic, mai shekara 24 cikin jerin sunayen ƴan wasan gaban da ta ke nazari a kai. (Football Insider)
Liverpool ta mai da hankali kan ɗaukar ɗan wasan gaban Brighton da Brazil Joao Pedro mai shekara 23 a bazara mai zuwa.(Universo Online)
Ƙungiyoyin Premier da dama na sanya ido kan ɗan wasan bayan Mozambique Reinildo mai shekara 30, wanda kwantiraginsa a Atletico Madrid zai ƙare a bazara mai zuwa. (Football Transfers)
Crystal Palace da Everton da Fulham duk suna zawarcin dan wasan gaban Lyon da Faransa Ernest Nuamah, mai shekara 21. (Foot Mercato)
Manchester United ba ta cikin gaggawar kawo wanda zai maye gurbin Dan Ashworth kuma ta yi imanin cewa ta na da ƙwararrun shugabannin da za su iya gudanar da ayyukansa a cikin ɗan gajeren lokaci, har ma a matsayin dindindin. (Teamtalk)
Bayan tafiyar Ashworth, darektan fasaha na Manchester United Jason Wilcox zai iya kula da harkokin kulob ɗin a kasuwar musayar ƴan wasa ta watan Janairu, yayin da ake neman wanda zai maye gurbinsa. (Daily Mail)
Juventus na nazarin yiwuwar ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Chelsea Cesare Casadei a matsayin aro. Ana alaƙanta ɗan ƙasar Italiyan mai shekaru 21 da ƙungiyar Monza ta gasar Serie A. (Calciomercato)
Ɗan wasan tsakiya na Newcastle United da Italiya Sandro Tonali na da niyyar komawa Serie A, amma tafiya a watan Janairu zai kasance a matsayin aro saboda girman albashin ɗan wasan mai shekaru 24. (Gazzetta dello Sport)
West Ham na tunanin ɗaukar aron wani ɗan wasan gaba a watan Janairu sakamakon raunin da ɗan wasan Jamaica Michail Antonio, mai shekara 34 ya ji. (GiveMeSport)
Wolves na son tsawaita kwantiragin ɗan wasan bayan Portugal, Nelson Semedo, mai shekara 31. (Express & Star)
Tottenham na ci gaba da tattaunawa don ɗaukar ɗan wasan gaba dan ƙasar Ireland Mason Melia mai shekaru 17 daga St Patrick's Athletic. (Football Insider)











