Hwang ya nemi afuwar bidiyon tsaraici da ya yi wa budurwsa a ɓoye

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Koriya ta Kudu Hwang Ui-jo ya nemi afuwar daukar bidiyon tsirar budurwarsa da ya yi a ɓoye.
Mai gabatar da ƙarar ya ce ɗan wasan gaban mai shekara 31 ya naɗi bidiyon biyu daga cikin 'yan matansa lokacin da suke tarayya ba tare da neman izininsu ba, hakan ya faru har sau hudu tsakanin watan Yuni zuwa Satumbar 2022.
A bayyanarsa ta farko da ya yi a gaban kotun da ke birnin Seol a yau Laraba, Hwang ya ne mi afuwa tare da nuna nadama da wannan aiki da ya yi.
Dan wasan ya bar kungiyar Nottingham Forest a watan jiya ya kuma koma Alanyarpor ta Turkiyya.
Bidiyoyin sun fito ne bayan ƙanwar matarsa ta wallafa su da nufin ɓata masa suna.
An ɗaure ta a gidan yari na tsawon shekara uku a watan Satumbar bayan samunta da laifin ɓata masa suna a ƙarar da ya shigar da ita.
Amma duk da haka an ci gaba da tuhumarsa na ɗaukar bidiyon ba bisa ƙa'ida ba.
Masu gabatar da ƙarar sun ƙi bayar da bayanai kan matan da ke cikin bidiyon domin kare su daga wani abu mai cutarwa a nan gaba.
"Ba zan ƙara wani kuskure ba a nan gaba kuma zan ci gaba da ƙoƙarina a matsayin ɗan kwallo," in ji Hwang
"Ina mai matuƙar bayar da haƙuri ga waɗanda na ɗauka bidiyon wanda abin da na yi ba daidai ba ya cutar da su, ina ba da hakuri ga mutanen da na ɓata wa rai daga masoyana," ya ƙara da cewa.










