Turpin ne zai busa wasan Real da Atletico a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon kafa ta Turai, Uefa ta bayyana, Clement Turpin wanda zai yi rafli a wasan Real Madrid da Athletico Madrid a Champions League ranar Talata.
Real za ta karɓi bakuncin Atletico a wasan hamayya a zagayen farko na ƴan 16 a gasar ta zakarun Turai a Santiago Bernabeu.
Wannan shi ne karo na tara da alkalin wasan ɗan kasar Faransa zai busa wasan da ya shafi Real Madrid a Champions League.
Cikin wasa takwasa da Turpin ya yi rafli, Real Madrid ta yi nasara bakwai da canjaras ɗaya.
A wasan na ƴan birnin Madrid, an kara sau bakwai tsakanin Real da Atletico a gasar zakarun Turai shida da Europen Super Cup ɗaya.
Real ta yi nasara a Champions League uku da canjaras biyu, Atletico ta ci wasa biyu har da a European Super Cup da ta ci 4-2 ranar Laraba 15 ga watan Agusta 2018.
Atletico Madrid tana ta biyu a teburin La Liga da maki 56 da tazarar maki ɗaya tsakani da Barcelona mai jan ragama.
Real Madrid mai maki 54 tana mataki na uku a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya, bayan kammala wasannin mako na 26.
Wasannin da Turpin ya busa na Real Madrid:
- Real Madrid 4-0 Ludogorets (2014/15 wasannin cikin rukuni)
- Roma 0-2 Real Madrid (2018/19 wasannin cikin rukuni)
- Real Madrid 3-2 Inter Milan (2020/21 wasannin cikin rukuni)
- Chelsea 1-3 Real Madrid (2021/22 kwata fainal zagayen farko)
- Liverpool 0-1 Real Madrid (2021/22 wasan karshe)
- Napoli 2-3 Real Madrid (2023/24 wasannin cikin rukuni)
- Bayern Munich 2-2 Real Madrid (2023/24 daf da karshe zagayen farko)
- Manchester City 2-3 Real Madrid (2024/25 wasan cike gurbin shiga ƴan 16)












