Waiwaye: Saya wa Tinubu sabon jirgi da kisan sarkin Gobir

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Wannan maƙala ce da ke duba kan muhimman labaran da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata

'Yan bindiga sun kashe Sarkin Gobir bayan garkuwa da shi

Marigayi sarkin Gobir

Asalin hoton, Zazzau Emirate Photograper

Babban labarin da ya fi tayar da hankali cikin mako da muke bankwana da shi, shi ne labarain kisan Sarkin Gobir na Gatawa, Alhaji Isah Bawa da 'yan bindiga suka yi bayan garkuwa da shi na tsawon makonni.

A ƙarshen makon da ya gabata ne aka ga sarkin a wani bidiyo yana neman gwamnatin jihar Sokoto ta biya 'yan bindigar kuɗin fansar da suka buƙata, inda ya ce idan wa'adi ya cika ba a biya ba za su halaka shi.

Lamarin ya faru ne mako uku bayan 'yan bindigar sun yi garkuwa da sarkin a yankin Kwanar Maharba lokacin da yake kan hanyar komawa gida bayan halartar wani taro a cikin garin Sokoto.

Labarin kisan sarkin ya ja hankali sosai a Najeriya, inda shugaban asar Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan sarkin tae da umartar sojojin ƙasar su, su binciko waɗanda suka kashe sarki.

Shugaban Najeriya ya sayi sabon jirgi

An ƙiyasta darajar sabon jirgin na shugaban Najeriya kan dala miliyan 600

Asalin hoton, State House

Bayanan hoto, An ƙiyasta darajar sabon jirgin na shugaban Najeriya kan dala miliyan 600

A farkon makon ne kuma shugaban Najeriya, Bola Tinubu fara amfani da sabon jirgin da ya saya.

Labarin sayen sabon jirfin dai ya ɓulla a lokacin da shugaban ya yi bulagura zuwa ƙasar Faransa cikin makon

A ranar Litinin ne Shugaba Tinubu hau jirgin na Airbus A330 zuwa Faransa, wanda shi ne mafi sabunta cikin tawagar jiragen shugaban ƙasar da suka zarta biyar.

Sai dai babu tabbas ko majalisun dokokin ƙasar sun amince da sayen jirgin ganin cewa ba a sani ba ko yana cikin kasafin kuɗin ƙasar na 2024, kuma ba a bayyana kuɗin da aka kashe wajen sayensa ba.

Matakin na zuwa ne ƙasa da mako biyu bayan zanga-zangar da 'yan ƙasar suka yi kan tsadar rayuwa.

Kudirat Kekere-Ekun ta zama babbar Mai shari'a ta Najeriya

Kudirat Kekere-Ekun

Asalin hoton, Supreme Court

A ranar Juma'a shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya rantsar da Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin mai riƙon muƙamin Babbar Mai Shari'a ta ƙasar.

A yanzu Kekere-Ekun ta maye gurbin Mai shari’a Olukayode Ariwoola, wanda ya yi ritaya bayan ya kai shekara 70 a duniya.

An gudanar da bikin rantsarwar ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

A makon da ya gabatan ne Hukumar Kula da Harkokin Shari'a ta Najeriya (NJC) ta gabatar da sunanta ga shugaban na Najeriya domin amincewa tare da naɗa ta kan muƙamin.

Za mu tsayar da Najeriya cak idan aka kama shugabanmu - NLC

Shugabannin NLC

Asalin hoton, NLC

Bayanan hoto, Shugabannin NLC

A makon ne kuma Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya NLC, ta yi gargaɗi tare da yin barazanar fara yajin aikin sai baba-ta-gani, idan har aka kama shugabanta, Joe Ajaero.

Ƙungiyar ta yanke wannan shawarar ne bayan gayyatar da rundunar ƴansandan Najeriya ta yi wa shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, wanda ta ce hakan na da alaƙa ne da bincikensa da ake yi kan zargin samar da kuɗade domin tallafa wa ayyukan ta'addanci, da aikata laifuffuka ta shafukan intanet, da zamba, da haɗa baki wajen aikata laifuka da kuma cin amanar ƙasa.

Sai dai a nata ɓangaren, NLC ta bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe kuma ta yi zargin cewa lamarin na da alaƙa da siyasa.

Mutum 12 sun mutu bayan shan miyar lalo a Zamfara

A farkon makon ne kuma mutum 12 suka mutu a garin 'Ɗaki Takwas da ke ƙaramar hukumar Anka ta Jihar Zamfara, bayan sun sha wata miyar ganyen lalo mai ɗauke da sinadarin maganin kashe 'kwari.

Mutum 25 ne da suka fito daga gidaje biyu suka sha miyar a ranar Juma'a inda tun a lokacin suka fara rasuwa ɗaya bayan ɗaya.

Daraktan Kula da Lafiyar Al'umma kuma jami'i mai Kula da cututtuka masu yaɗuwa a jihar, Dakta Yusuf Abubakar Haske ya tabbatar wa BBC cewa shan miyar da aka yi da ganyen lalon ce ta yi sanadiyar mutuwar mutanen.

Lamarin na zo ne kwanaki biyu bayan wasu mutum shida 'yan gida guda sun mutu sakamakon shan gishirin ƙunshi a miya a jihar Sokoto mai makwabtaka

Wale Tinubu ba shi da hannun jari a kamfanin da muka saya - NNPCL

Kamfanin NNPCL

Asalin hoton, NNPCL/X

A makon da muke bankwanan da shi ɗin ne kuma babban kamfanin mai na gwamnatin Najeriya, NNPCL, ya musanta zarge-zargen da tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya yi cewa sayen kamfanin mai na OHV da NNPCL ya yi wani yunƙuri ne da shugaban ƙasar ke yi na shigar da harkokin kasuwancinsa cikin dukiyar gwamnati.

Cikin wata sanarwa da babban jami'in sadarwa na kamfanin, Olufemi Soneye, ya fitar ya ce Shugaba Tinubu da Wale Tinubu babu ko ɗaya daga cikinsu da ke da hannu a sayen kamfanin na OVH.

''A lokacin da NNPCL ya sayi OVH a 2022, kamfamin Oando (wanda Wale Tinubu ke da hannayen jari a cikinsa), ya riga ya janye hannayen jarinsa a kamfanin OVH, daga masu kamfanin - Vitol da kuma Helios'', kamar yadda sanarwar ta yi bayani.