Manchester United ta tuntubi Real Madrid kan Casemiro

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United t tuntubi Real Madrid domin daukar dan was anta na tsakiya dan kasar Brazil Casemiro, cinikin da ake sa ran zai kai fan miliyan 60.
Dan wasan mai shekara 30 zai zama Daya daga cikin wadanda suka fi kowa yawan daukar kudi idan ya amince ya koma kungiyar da ke kasar teburin gasar Peremier.
Bayan gazawar da tattaunawa tsakani Juventus da United ta yi kan bukatar danb wasa Adrien Rabiot, yanzu kungiyar ta karkata Casemiro wanda ake ganin inda yake bugawa ne matsalar da kocin Erik ten Hag ke da ita a yanzu.
Dan wasan Brazil din ya koma Real Madrid ne tun a 2013, ya kuma lashe kofin La Liga uku da gasar Champions biyar.
Duk da cewa kwantaragin dan wasan za ta kare ne a 2025, amma Real na ganin za ta iya kara tsawaita kwantaraginsa zuwa 2027 da zarar ta tattauna hakan da dan wasan.
Da yiwuwar dan wasan ya koma Manchester United, idan aka yi la’akari da barazanar da zai fuskanta daga sabon dan wasan da Real ta saya, Aurelien Tchouameni.
Casemiro ya taba yin kaka daya ba a Bernabeu ba, lokacin da yaje kungiyar Porto ta Portugal a matsayin aro a 2014/15.
Ya buga wa Real wasanni 222 kuma ya ci mata kwallo 24 ya zuwa yanzu.









