'Yan sanda sun ja kunnen Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

'Yan sanda sun ja kunnen Cristiano Ronaldo, bisa wani faifan bidiyon da ya nuna dan kwallon ya wafce wayar dan kallo ya buga da kasa.

'Yan Sandan Merseyside sun ce sun yi wa dan wasan mai shekara 37 tambayoyi, sun kuma gargadeshi kan laifin da ya shafi cin zarafi da lalata dukiya.

Jami'an tsaron sun tabbatar da faruwar lamarin sun kuma damu da halayar a karawar da United ta yi da Everton ranar 9 ga watan Afirilu.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila itama ta ce za ta gudanar da nata binciken nan gaba.

Bayan da lamarin ya faru dan kwallon Manchester United ya kai kansa wajen 'yan sanda - ya kuma nemi afuwa a kafar sada zumunta kan abin da ya aikata.

Ya kuma gayyaci matashin zuwa Old Trafford, domin ganin wasan Manchester United nan gaba.

'Yan sandan sun gudanar da bincike, bayan wani faifan bidiyo da ya karade kafar sada zumunta da ya nuna Ronaldo ya wafce wayar wani dan kallo ya buga ta da kasa.

Ronaldo ya harzuka a wasan da United ta yi rashin nasara da ci 1-0 a gasar Premier League a Goodison Park.

Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce sun ja kunnen dan kwallon tawagar Portugal, sun kuma kawo karshen lamarin.