Real za ta dauki Kane, wanda United da Bayern ke son saya

An wallafa

Real Madrid na bibiyar halin da ake ciki a Tottenham, bayan da yarjejeniyar Harry Kane zai kare a kungiyar a kakar 2024.

Tuni ake alakanta dan wasan da cewar Manchester United ko kuma Bayern za ta sayi dan kwallon tawagar Ingila. (Mail)

Manchester City za ta kara kudin kwantiragin Erling Haaland ga duk kungiyar da ke son daukar dan wasan, wanda yanzu yake fam miliyan 175, wanda yarjejeniyarsa zai kare a Etihad a 2027. (Goal)

Dan wasan Chelsea, Mason Mount, mai shekara 24, ya dauki sabon wakili da zai yi masa aikin samar masa wata kungiya, domin ya bar Stamford Bridge. (Mail)

Dan kwallon Paris St-Germain da tawagar Argentina, Lionel Messi, mai shekara 35 na son koma wa Barcelona da taka leda karkashin koci, Xavi. (Foot Mercato - in French)

Brighton za ta kara kudin yarjejeniyar dan kwallon tawagar Japan, Kaoru Mitoma, mai shekara 25, wanda zai zama mafi tsada a kungiyar, bayan da Real Madrid da Manchester City da Arsenal ke son daukar dan wasan. (Goal)

Arsenal za ta sake sabon taya dan wasan Brighton, Moises Caicedo duk da cewar kwanan nan ya saka hannu kan kwantiragin ci gaba da taka leda a kungiyar. (Football Insider)

Sevilla ba za ta dauki dan wasan Manchester United, Alex Telles, wanda ke buga mata wasannin aro a kungiyar ba. (Mirror)

An kori Patrick Vieira daga horar da Crystal Palace, bayan da kungiyar ke hangen baya matsawa 'yan wasansa. (Mirror)

Chelsea na mutukar son daukar dan wasan West Ham, Declan Rice, mai shekara 24 a karshen kakar nan, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a 2024. (Florian Plettenberg)

N'Golo Kante, mai shekara 31 - wanda rabon da ya buga wa Chelsea tamaula tun cikin watan Agusta, na daf da tsawaita zamansa a Stamford Bridge. (Sun)

Dan wasan Barcelona, Frenkie de Jong, wanda Manchester United da Chelsea ke son dauka ya fada a wata hira a talabijin cewar zai ci gaba da taka leda a Camp Nou. (TV3 - in Catalan)

Dan kwallon Najeriya, Alex Iwobi, mai shekara 26, wanda yarjejeniyarsa zai kare a Everton a 2024, an yi masa tayin sabon kwantiragin tsawaita zamansa. (Football Insider)

Liverpool za ta amince Alex Oxlade-Chamberlain da Naby Keita su bar kungiyar a karshen kakar nan. (Athletic - subscription required)

Dan kwallon Bayern Munich, Ryan Gravenberch, mai shekara 20, ya kulla yarjejeniyar komawa Liverpool da taka leda in ji tsohon dan wasan kungiyar Anfield, Jose Enrique. (Sun)

Dan wasan Napoli, Khvicha Kvaratskhelia, wanda ake alakanta shi da zai koma Real Madrid ko Manchester City, watakila Newcastle ta dauki shi idan ta samu gurbin buga Champions League a badi. (Football Insider)

Watakila Barcelona ta sayar da Ousmane Dembele da Ferran Torres domin ta samu kudin sayen dan kwallon Juventus, ederico Chiesa, mai shekara 25. (Calciomercato - in Italian)

Barcelona ta yi wa Sergio Busquets tayin kwantiragin kaka daya domin ya ci gaba da taka leda a Camp Nou da yarjejeniyar tsawaita masa kaka daya, ana kuma cewar watakila zai koma wasa a Inter Miami ko kuma Toronto, wasu na cewar kungiyoyi uku a Saudi Arabia na son sayen shi. (Mundo Deportivo - in Spanish)