Kane ya kafa tarihin cin kwallaye da yawa na kashin kansa

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Harry Kane ya kafa tarihin yawan cin kwallo 31 a lik, bayan da Bayern Munich ta je ta doke Darmstadt 5-2 ranar Asabar a Bundesliga.

Hakan ya sa Bayern ta rage tazarar makin dake tsakaninta da mai jan ragamar teburi, Bayern Leverkusen yanzu ya koma saura bakwai.

Darmstadt ce ta fara cin kwallo ta hannun Tim Skarke daga baya Jamal Musiala ya farke.

Kane ne ya ci wa Bayern na biyu, sannan Musila ya kara na uku na biyu da ya zura a raga a fafatawar.

Serge Gnabry da Mathys Tel ne suka ci wa Bayern sauran kwallaye da suka cika biyar a ragar.

Yayin da Oscar Vilhelmsson ya kare zare daya a wasan da aka doke Darmstadt 5-2 a fafatawar ta Bundesliga.

An yi fargabar ko Kane, dan wasan tawagar Ingila ya ji rauni a zagaye na biyu, bayan da ya yi karo da turken raga.

An canja Kane saura minti takwas a tashi a wasan kuma kociyan Bayern, Thomas Tuchel bai yi karin bayani ba kan girman raunin tsohon dan wasan Tottenham ba.

Harry Kane

Asalin hoton, Getty Images

Kane ya taba cin kwallo 30 a kakar tamaula a lokacin da yake Premier League a Tottenham.

Ya kuma kafa tarihin zura kwallaye da yawa a Bundesliga a kakarsa ta farko, wanda ke rke da tarihin shi ne Uwe Seeler mai 30 a kungiyar Hamburg a 1963-64.

Zai ziyarci Ingila a gasar Champions League zagayen kwata fainals a karawa tsakanin Bayern Munich da Arsenal - ya ci kwallo 14 a wasa 19 da ya fuskanci Gunners.

Bayern za ta fara zuwa Emirates ranar 9 ga watan Afirilu, su buga fafatawa ta biyu a Jamus ranar 17 ga watan Afirilu.