Ƙungiyoyin Premier na rububin sayen Benjamin Sesko

Benjamin Sesko

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Benjamin Sesko ya ci wa RB Leipzig ƙwallo 17 a kakar bana
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗanwasan gaba na RB Leipzig, Benjamin Sesko, na ci gaba da jan hankalin ƙungiyoyin gasar Premier League ta Ingila yayin da yake shirin barin kulob ɗin a ƙarshen kakar wasa ta bana.

Kafar yaɗa labarai ta Sky a Jamus ta ruwaito cewa ƙungiyoyin Arsenal, da Chelsea, da Manchester United, da Tottenham duka sun nuna sha'awar ɗaukar ɗanwasan mai shekara 21.

Arsenal ta kwana biyu tana neman Sesko ɗan ƙasar Slovenia. Sai dai ya tsawaita zamansa a Leipzig har zuwa 2029 kafin fara kakar wasa ta bana.

Duk da cewa an fitar da ƙungiyar tasa daga gasar Champions League ta bana, tana matasayi na shida a teburin gasar Bundesliga ta Jamus.

Kafar Sky ta ruwaito cewa ƙunshin yarjejeniyarsa ta tanadi yuro miliyan 75 a matsayin farashinsa, amma akwai yiwuwar zai iya kaiwa har milyan 80.

Sesko ya ci ƙwallo tara a wasa 23 da ya buga a Bundesliga ta bana bayan ya ci 14 a kakar bara, inda yanzu yake da jimillar 17 a raga a kakar ta bana.