Kociyoyin Ghana suna murmurewa bayan haɗarin mota

Ghana

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kociyan tawagar kwallon kafa ta Ghana uku suna samun sauki har da tsohon ɗan wasan Premier League, John Paintsil bayan haɗarin mota.

Koci, Otto Addo da mataimakinsa Paintsil da mai horar da masu tsaron raga, Fatawul Dauda sun yi haɗarin ne a lokacin da suke kan hanyar komawa gida, bayan zuwa kallon wasa a ƙungiyoyin Ghana, domin tsintar karin ƴan wasa.

Motarsu ta yi damaji a lokacin da suka yi kokarin kaucewa wata karamar mota mai buɗaɗɗen baya, wadda ta faɗa ɗaya hannun masu tafiya.

Hukumar ƙwallon kafa ta Ghana na fatan za su murmure, domin jan ragamar wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka da za ta yi da Angola ranar Alhamis da Niger ranar Litinin.

Paintsil, mai shekara 43, ya buga wa West Ham da Fulham da kuma Leicester City tamaula tsakanin 2006 zuwa 2012.

Addo tsohon ɗan wasan Borussia Dortmund, mai shekara 49, yana kan aikin horar da tawagar Black Stars a karo na biyu.

A jawabin da hukumar ƙwallon kafa ta Ghana ta fitar ''Sun je aiki ne domin kallon zakaru biyu tsakanin FC Samartex 1996 da kuma Nsoatreman FC.