Cubasi zai ci gaba da taka leda a Barca zuwa 2029

Pau Cubarsí

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Barcelona, Pau Cubarsi ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a ƙungiyar zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2029.

Mai tsaron bayan ya rattaba hannu kan ƙwantiragi a gaban shugaban Barcelona, Joan Laporta da mataimaki na farko, Rafa Yuste da daraktan tamaula, Anderson Luis de Souza "Deco".

Wannan yarjejeniyar ta nuna yadda Barcelona ke ɗaga darajar matasan ƴan wasanta da take rena daga La Masia.

Koda yake Barcelona na fama da matsin tattalin arziki, wadda ta lashe Spanish Super Cup a Saudiyya a cikin watan Janairu, bayan doke Real Madrid.

Cubarsi bai daɗe da yin bikin cika shekara 18 da haihuwa ba, yanzu ya buga wa babbar ƙungiyar Barcelona tamaula karo 60.

Ya fara yi mata tamaula a Copa del Rey a fafatawa da Unionistas ranar 18 ga watan Janairu a Salamanca a 2024.

A kakar nan ya buga wa Barcelona wasa 36 ciki har da La Liga da Champions League da Spanish Super da kuma Copa del Rey.

Mai tsaron baya ne mai cike da koshin lafiya, wanda ya karɓi katin gargadi huɗu daga karawa 36 da ya yi wa Barcelona a kakar nan.