Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar: Neymar, Eriksen, Dembele, Traore, Dennis, Asensio, Lingard, Ekitike

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan gaba na Brazil Neymar, mai shekara 30, na duba yiwuwar barin Paris St-Germain a wannan kakar, bayan samun labarin da ke cewa kulob din zai bar shi ya tafi. A bangare guda kuma kungiyar Chelsea na tuntubar wakilinsa domin daukar dan wasan. (ESPN)
Manchester United za ta kammala magana da Christian Eriksen kuma tuni batun ya yi nisa da dan wasan tsakiya na Denmark mai shekara idan kwantiraginsa da Brentford yak are. (Star)
Chelsea, Paris St-Germain da Bayern Munich na matsa kaimin daukar dan wasan gaba na Faransa da Barcelona Ousmane Dembele, mai shekara 25. (Marca)
Barcelona ta yanke shawara kan tsohon dan wasan Wolves da Sifaniya Adama Traore dan shekara 26, kan kwantiragi maimakon aro . Barca dai na da aniyar rattaba hannu kan daukar dan wasa Traore kan farashin yuro miliyan 30 (£26m). (Sport)
Dan wasan Watford da Najeriya mai kai hari, Emmanuel Dennis, dan shekara 24, na cikin jerin wadanda Everton take son dauka domin maye gurbinsa da dan wasan gaba na Brazil mai shekara 25, Richarlison, wanda ya tafi Tottenham kan fam miliyan 60. (Evening Standard)
Dan wasan Real Madrid kuma na tsakiyar Sifaniya Marco Asensio, mai shekara 26, ka iya barin Bernabeu a kakar wasan bana, idan Real ba su yi masa tayin tsawaita kwantiraginsa ba, wanda zai kare a shekara mai zuwa. AC Milan na daga cikin masu zawarcin dan wasan, duk da cewa wasu daga cikin kulob-kulob din Premier League sun fara nuna shawa’a kan daukarsa. (Marca)
Tottenham da West Ham, Everton da Newcastle United na cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan tsakiyar Ingila, Jesse Lingard, dan shekara 29, bayan ya bar Manchester United sakamakon karewar kwantiraginsa. (Telegraph, subscription required)
Tottenham sun kusa kammala Shirin daukar dan wasan Barcelona mai tsaron gidan Faransa, Clement Lenglet, mai shekara 27, duk da cewa makomar dan wasan baya na Brazil Emerson Royal tana-kasa-tana-dabo kan komawarsa Atletico Madrid. (Express)
Dan wasan baya na Sifaniya, Hector Bellerin, mai shekara 27, na atisaye bayan musayarsa da aka yi daga Arsenal zuwa Real Betis. Bellerin ya ce ya koyi abubuwa da dama a lokacin da ya ke Betis, hakan ya taimaka masa wajen sake kaunar wasanni. (Star)











