Arsenal na son Monga, Xhaka ya dage kan Chelsea, Diomande ya zabi PSG kan Liverpool

Diomande

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Ɗan wasan gefen Ivory Coast, Yan Diomande, ya bayyana cewa PSG ce zaɓinsa na farko idan ya yanke shawarar barin RB Leipzig a kakar bazara mai zuwa. Wannan na zuwa ne duk da cewa manyan kungiyoyi irin su Liverpool da Real Madrid suka nuna sha'awar daukar matashin dan wasan mai shekaru 19. (Athletic - subscription required, external)

Ɗan wasan tsakiyar Manchester United, Mason Mount, mai shekaru 27, an yi wa AC Milan tayin sa domin yiwuwar sake haɗuwa da tsohon kocin United, Rúben Amorim, (MilanPress - in Italian)

Chelsea na duba yiwuwar daukar Pep Chavarría, ɗan wasan bayan Spaniya na Rayo Vallecano mai shekaru 28, domin ya maye gurbin Marc Cucurella, wanda ya koma Real Madrid. (Marca - in Spanish, external)

Nottingham Forest na harin Curtis Jones, dan wasan tsakiyar Liverpool dan Ingila, inda kungiyar ke hasashen farashin dan wasan mai shekara 25 zai iya kai fam miliyan 40. (Talksport, external)

Arsenal na shirin ƙara ɗaukar sababbin 'yan wasa biyar a lokacin musayar 'yan wasa ta bazara inda daga cikinsu akwai matashin ɗan wasan gefen Leicester City, Jeremy Monga, ɗan Ingila mai shekaru 16.(Star, external)

Ɗan wasan tsakiyar Monaco, Maghnes Akliouche, ya shaida wa Liverpool da Manchester United cewa burinsa na farko a wannan bazarar shi ne komawa Paris Saint‑Germain (PSG), (Teamtalk).

Newcastle United ta ce har yanzu bata samu wata tuntuba ba akan dan wasan tsakiyarta Bruno Guimarães, duk da rahotannin da ke danganta ɗan wasan dan kasar Brazil mai shekaru 28 da komawa Arsenal.(Chronicle, external)

Aston Villa na bayam Leeds United wajen neman ɗan wasan Japan mai shekaru 23, Zion Suzuki, daga ƙungiyar Parma da ke buga gasar Serie A ta Italiya.(Calciomercato - in Italian, external)

Dan wasan bayan Chelsea, Malo Gusto, ya amince ya koma Manchester City, yayin da ɗan wasan Faransa mai shekaru 23 ke neman sake haɗuwa da tsohon kocinsa Enzo Maresca.(Footmercato - in French, external)

Yiwuwar komawar dan wasan tsakiyar Sunderland Granit Xhaka zuwa Chelsea na kara karfi, inda dan wasan ke karfafa maganar saboda sha'awarsa ta rayuwa a London da kuma son sake haduwa da Xabi Alonso, wanda ya taba aiki dashi a matsayin mai horarwa a lokacin da ya ke kungiyar Bayer Leverkusen. (Fabrizio Romano, external)

Juventus sun saka mai tsaron ragar Argentina kuma ɗan wasan Aston Villa, Emiliano Martínez, mai shekaru 33, cikin jerin 'yan wasan da suke son ɗauka a kakar bazara.(Tuttomercatoweb - in Italian)