Yadda yarjejeniyar ibada a masallacin Qudus ke cikin barazana

Wani Musulmi yana addu'a a gaban masallacin al-Aqsa a lokacin watan Ramadan, 2025.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Hasumiyar masallacin al-Aqsa da aka yi wa kwalliya da zinari
    • Marubuci, Wyre Davies
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East Correspondent
    • Aiko rahoto daga, Jerusalem
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

"Isra'ila baki ɗaya alƙawarin Allah ce ga ɗiyansa a duniya... kuma a nan ne za mu gina sabon wajen ibada ga dukkan mutanen duniya, inda za su zo su yi bauta tare.''

Waɗannan ne kalaman masu sarƙaƙiya Moshe Feiglin, ɗan siyasar Isra'ila mai ra'ayin mazan jiya, wanda ya zanta da ni a lokacin da fitowa daga harabar masallacin al-Aqsa da ke birnin Ƙudus, inda ya ɗauki lokaci yana rera waƙoƙin ibada tare da wasu Yahudawa 20 a cikin masallacin.

Feiglin ya yi maganar ne a fili kuma babu wani ɓoye-ɓoye, tamkar maganar tshi ba ta da alamar tambaya ko jayayya.

Amma a zahiri abin da ya ke cewa da kuma aikatawa abubuwa ne masu ruɗani kuma waɗanda ke iya janyo rikici da kuma kawo cikas ga yarjejeniyar da aka ƙulla a ɗaya daga cikin wuraren bauta mafi muhimmanci a doron ƙasa.

Ga Moshe Feiglin da sauran masu irin tunanin shi, abu ne mai sauƙi. Suna son gina sabon katafaren wajen bautar Yahudawa a wajen da ya kasance ɗaya daga cikin wuraren mafi muhimmanci ga mabiya addinin musulumci tsawon fiye da shekara 1,400 - alAqsa.

Musulmai na kiran harabar masallacin al-Haram al-Sharif yayin da Yahudawa ke masa laƙabi da Temple Mount, kuma ya kasance ɗaya daga cikin wurere masu daraja da tarihi a Gabas ta Tsakiya.

An ambaci Al-Aqsa a cikin Al-ƙur'ani kuma a musulumci an yarda cewa daga nan ne Annabi Muhammad ya tashi zuwa sama. Waje da aka keɓe domin sallah da ibada ga musulmai – ko hakan na shirin canzawa ne?

Moshe Feiglin lokacin da ake zantawa da shi

Asalin hoton, Maarten Lernout/BBC

Bayanan hoto, Moshe Feiglin

Wannan waje yana da amfani da daraja sosai ga Yahudawa. A ƙarƙashin ginin daga katangar Yamma, Yahudawa na taruwa su yi addu'a da jimamin yadda Rumawa suka rusa wajen bautar su shekaru dubu biyu da suka gabata.

A bisa yarjejeniyar da aka ƙulla shekaru aru-aru, an miƙa ragamar kula da al-Aqsa ne ga musulman Jordan.

An amince wa waɗanda ba musulmai ba su ziyarci al-Aqsa amma ba a amince su yi ibada a ciki ba.

Waɗannan yarjejeniya da ƙa'ida na daga cikin abubuwan da a yanzu Feiglin da sauran su ke yin facali da su ƙarara.

'Cibiyar addinai da dama'

Rahotannin baya-bayan nan da ke cewa Isra'ila da Amurka na aiki tare domin watsi da waccan yarjejeniya sun janyo fargaba.

Kafar yaɗa labarai ta Middle East Eye, ta ruwaito cewa majiyoyi da dama sun tabbatar mata cewa gwamnatin Isra'ila ta wata hukuma da za ta ayyana al-Aqsa a masatyin wajen bauta na addinai da dama.

Da aka tambaye shi a wajen wani taron jin bahasi na majalisar dokoki, sakataren harkokin wajen Amura Marco Rubio ya ce ba shi da wani labari a kai. Amma jakadan Amurka a Isra'ila, Mike Huckabee ya sha yin magana a kai, yana mai cewa Yahudawa na da alaƙa da wurare masu tsarki na birnin Ƙudus da kuma gaɓar yamma da kogin Jordan.

Wasu rahotannin na cewa za a riƙa barin tawagar Yahudawa shiga ciki domin yin ibada kuma a hankali Yahudawa za su ƙwace ikon gudanar da masallacin.

Ofishin firaminista ya sha nanata cewa babu wani sauyi da za a yi wa yarjejeniyar.

Dr Mustafa Abu Sway sanye da baƙar riga da farin rawani

Asalin hoton, Maarten Lernout/BBC

Bayanan hoto, Dr Mustafa Abu Sway ya ce sauya yarjejeniyar neman rigima ne

Dr Mustafa Abu Sway, mataimakin shugaban kwamitin shura ya yi gargaɗin cewa "Ba za ta saɓu ba,"

Ya bayyana gfargabar cewa duk wani yunƙuri na sauya yarjejeniyar zai iya rura wutar rashin jituwa tsakanin Yahudawa da Musulmai.

"Zaman lafiya ba tare da janye duk wani yunƙurin mamaye masallacin al-Aqsa ba tamkar neman faɗa ne. Mataki ne na janyo tashin hankali a yankin, in ji Abu Sway.

Damuwar ƙasashen duniya

Jordan da ƙasashen yankin Gulf da kuma Masar sun bayyana damuwa kan ƙwace iko da al-Aqsa daga hannun hukumomin musulumci. Itama gwamnatin Birtaniya ta ce dole ne a mutumta yarjejniyar da aka ƙulla a kan wajen.

Minsitan tsaron Isra'ila, Itamar Ben-Gvir, ya ce ''The Temple Mount namu ne,'' Ya yi wannan magana ne a wani gangami da suka yi a sassan birnin Ƙudus.

Itamar Ben-Gvir ya yi amfani da matsayin shi wajen  bai wa Yahudawa damar gudanar da ibada a harabar masallacin.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Itamar Ben-Gvir ya yi amfani da matsayin shi wajen bai wa Yahudawa damar gudanar da ibada a harabar masallacin.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mutumin mai yawan ruɗani wanda ke cikin gwamnatin haɗaka ta Benjamin Netanyahu ya kasance mai yawan ziyartar al-Aqsa.

An ga wani bidiyo inda yake ɗaga tutar Isra'ila yayin da yake rera waƙa, wani abu da ya yi hannun riga da tanadin yarjejeniyar.

Fiye da shekara 25 baya, a cikin watan Satumban 2000, ɗan siyasar Isra'ila mai ra'ayin mazan jiya, Ariel Sharon ya yi abin da ba a taɓa zato ba. Ya jagoranci tattakin ɗaruruwan ƴansandan Isra'ila ɗauke da makamai, da jagoran ƴan adawa inda suka shiga har harabar al-Aqsa.

Da dama ana ganin matakin nasa a matsayin yunƙurin tayar da rikici kuma ɗaya daga cikin abubuwan da suka tunzura rikicin Falasɗinu da ake kira rikicin al-Aqsa. Shekaru biyar da suka biyo baya an kashe mutane fiye da dubu huɗu a tashin hankalin daaka yi a Isra'ila da gaɓar yamma da kogin Jordan da kuma Zirin Gaza.

Abu ne mai wahala a yi hasashen abin da zai faru idan aka yi yunƙurin ƙwace iko a gini mai matuƙar muhimmanci da daraja ga ɗimbin mabiya addini.