Ronaldo da Messi za su buga Gasar Kofin Duniya karo na biyar

Asalin hoton, Getty Images
Lionel Messi da Cristiano Ronaldo za su buga Gasar Kofin Duniya karo na biyar a tarihi a Qatar da za ta karbi bakuncin daga 20 ga watan Nuwamba.
Kyaftin din Argentina da na Portugal na hamayya da juna wajen bajintar taka leda da cin kwallaye da lashe lambar yabo a tsakaninsu a tamaula.
Hamayyarsu ta yi kamari a lokacin da Messi ke wasa a Barcelona da Ronaldo a Real Madrid, yanzu Messi na Paris St Germain da Ronaldo ke Manchester United.
Watakila wannan Gasar ita ce ta karshe a tsakaninsu da za su buga, wannan dama ce da za su karkare hamayya a tsakaninsu a babbar gasar tamaula ta duniya.
Messi da Ronaldo ba wanda ya taba cin kofin duniya, saboda haka wannan ce dama ta karshe da ya kamata wani daga ciki ya dauki kofin don yi wa daya fintinkau.
Messi wanda zai buga Gasar Kofin Duniya karo na biyar ya yi wasa 19 da cin kwallo shida da bayar da biyar aka zura a raga.
Shi kuwa Ronaldo mai karawa 17 ya zura kwallo bakwai a raga, sannan ya bayar da biyu aka ci a Gasar Kofin Duniya hudu da ya je a tarihi.
To sai dai Ronaldo na fatan kafa tarhin cin kwallo a gasar biyar a jere, bayan da ya zura kwalla a kowacce daga hudun da ya yi a baya.
Jerin gasar kofin duniya hudu da Messi da Ronaldo suka je a jere:
- Jamus 2006
- Afirka ta Kudu a 2010
- Brazil a 2014
- Rasha a 2018











