Wa zai kai wasan ƙarshe tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu?

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Najeriya za ta kara da Afirka ta Kudu ranar Laraba a wasan daf da ƙarshe a gasar kofin Afirka da ake yi a Ivory Coast.
Super Eagles ta kawo wannan matakin bayan da ta yi ta biyu a rukunin farko da maki bakwai.
Sai Najeriya ta ci Kamaru 2-0 a karawar zagaye na biyu na ranar 27 ga watan Janairu, sannan ta ci Angola 1-0 a kwata fainal ranar 2 ga watan Fabrairu.
Ita kuwa Afirka ta Kudu ta yi ta biyu a rukuni na biyar da maki huɗu, sai kuma ta fitar da Morocco da ci 2-0 a zagaye na biyu ranar 30 ga watan Janairu.
Bafana-Bafana ta kai daf da ƙarshe ne, bayan da ta doke Cape Verde 2-1 ranar 3 ga watan Fabrairu.
Abubuwan da suka kamata ku sani kan wasa tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu.
- Wannan shi ne wasa na huɗu da za su fuskanci juna a Afcon, inda Super Eagles ta yi nasara a uku da cin kwallo 8-1.
- Wasa na ƙarshe da suka kara da juna a zagayen daf da ƙarshe a Afcon shi ne a 2000, inda Najeriya ta yi nasara da cin 2-0 ta hannun Tijjani Babangida.
- Najeriya za ta buga a matakin daf da ƙarshe karo na 16 a gasar kofin Afirka, amma sau ɗaya ta kai karawar ƙarshe daga shida da ta buga na baya-bayan nan, shi ne wanda ta ɗauki kofin a 2013 a Afirka ta Kudu, kuma na uku jimilla.
- Super Eagles ta yi nasara a wasa huɗu a Afcon ta bana ba tare da ƙwallo ya shiga raga ba, wadda ke fatan yin na biyar a jere kuma a karon farko da za ta yi wannan ƙwazon tun Maris ɗin 1982, wadda ta yi nasara huɗu da canjaras ɗaya.
- Afirka ta Kudu za ta buga daf da ƙarshe karo na huɗu a Afcon, kuma na farko tun bayan 2000, bayan da Najeriya ta doke ta 2-0.
- Bafana-Bafana ta yi wasa huɗu a gasar bana ba tare da ƙwallo ya shiga ragarta ba da cin biyu da canjaras biyu, nasara mafi ƙyau da ta yi fiye da fafatawa 21 a baya a Afcon.
- Ƴan wasa uku ne suka ci wa Super Eagles ƙwallaye a Afcon 2023 da ya haɗa da Lookman da Osimhen da kuma Troost-Ekong, karon farko da ta yi ƙarancin masu cin ƙwallaye tun bayan 2008 da Yakubu da Mikel.
- Ƙwallo daya Victor Osimhen ya ci a bana duk da cewar ya kai hare-hare 19 a gasar ta Afcon 2023.
- Super Eagles ce kan gaba a yawan samun damar cin ƙwallo har karo 18 a Afcon 2023, wadda ta zura ƙwallo shida a raga a cikin da'ira. Afirka ta Kudu ce kan gaba da buga ƙwallo zuwa raga daga cikin da'ira sau 46, sai Najeriya mai 44.
- Themba Zwane yana da hannu a kwallo uku daga shida da Afirka ta Kudu ta ci a Afcon 2023, wanda ya zura biyu a raga ya bayar da ɗaya aka zura a raga. Watakila ɗan wasan Bafana-Bafana ya zama na farko da zai ci kwallo uku a kakar Afcon tun bayan 2000 da Shaun Bartlett ya zura biyar a raga.







