Tunisia ta ci Faransa amma ta yi ban kwana da Gasar Kofin Duniya

Asalin hoton, Getty Images
Tunisia ta ci Faransa 1-0 a wasa na uku a rukuni na hudu a Gasar Cin Kofin Duniya a Qatar, amma ba ta kai zagayen gaba ba.
Tunisia ta ci kwallon bayan da aka koma zagaye na biyu ta hannun Wahbi Khazri, tun farko Nader Ghandri ya ci Faransa, amma aka soke a minti na takwas.
Daga baya Faransa ta farke ta hannun Antoine Griezmann a filin wasa na Educational, amma na'urar da take taimakawa alkalin wasa ta yanke hukunci ta soke ta.
A daya wasan a rukuni na hudu Australia ta doke Denmark 1-0, hakan ya sa Tunisia ta yi ban kwana da Gasar Kofin Duniya da ake yi a Qatar.
Faransa mai rike da kofin ta kai zagayen gaba tun farkon da ta ci Denmark a wasan da ya gabata a karawa ta biyu a rukunin.
Autralia ma maki shida ne da ita iri daya da na Faransa, sai Tunisia mai hudu da kuma Denmark mai daya kwal.






