An kai marasa lafiya 500 asibiti mai gado biyar a Afghanistan bayan girgizar kasa

Afghanistan

Asalin hoton, Gayan Comprehensive Health Center

An wallafa

"Marasa lafiya 200 ne suka mutu a cikin 500 da aka kawo wannan asibitin."

Wannan shi ne kalamin da Muhammad Gul, wani ma'aikacin karamin asibiti da ke Gyan, a gabashin Afghanistan ya yi.

Gadaje biyar ne kacal a asibitin, kuma girgizar kasar da aka yi ranar Talata ta fito da matsalar rashin isassun gadaje a asibitocin kasar.

"Dukkan ɗakunan asibitocin sun lalace," a cewar Gul a hirarsa da BBC.

Ya ce helikwafta ya dauki wasu marasa lafiya daga yankunan karkara na lardin Paktika zuwa birane domin a yi musu magani.

Sannan likitoci biyu suna aiki a wani asibitin wucin-gadi domin duba mutanen da ba za su iya zuwa ko ina ba.

Sai dai babu isasshen fetur a cikin injin janareton da ke aiki, kuma har yanzu ba a kai taimakon da wasu lardunan suka yi alkawarin kai wa lardin na Paktika ba.

A gefe guda, mutanen da suka jikkata suna ci gaba da ƙaruwa.

"Akwai mutane da dama da ke bukatar kulawar likitoci. Ina tsammani ba za su iya kwana da rai ba," in ji Gul.

Afghanistan

Asalin hoton, Gayan Comprehensive Health Center

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Girgizar kasar mai karfi da ta kai lamba 6.1 a ma'aunin Richter ita ce mafi muni da ta auka wa Afghanistan a cikin shekaru ashirin.

Ta auka wa gabashin kasar da Talata da asubahi.

Ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 1,000 sannan ta jikkata fiye da mutum 1,500 more, kamar yadda wani jami'i a gwamnatin Taliban ya bayyana.

Sai dai ana tsammani adadin zai karu a yayin da ake ci gaba da tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Sannan yanayin wurin da lamarin ya faru ya hana masu aikin ceto gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Girgizar kasar ta faru ne a yankuna masu cike da tsaunuka da ke da gidaje marasa kwari, wadanda ba za su iya jure mata ba.

Daruruwan gidaje sun rushe sannan an samu zaftarewar laka.

Gyan na cikin yankunan da lamarin ya fi yin kamari. Har yanzu mutane suna makale a cikin baraguzan gine-gine.

Kungiyoyin bayar da agaji na kasashen duniya sun gina asibitoci a can a shekarun da suka wuce.

An gina su ne domin duba marasa lafiya da ke da kananan larurori kuma ana tura masu manyan larurori birane domin a duba lafiyarsu.

Ba su da sassan da ke kula da marasa lafiyar da ke buakatar agajin gaggawa.

An gina su ne domin duba marasa lafiya da ke da kananan larurori kuma ana tura masu manyan larurori asibitocin da ke birane

Asalin hoton, Gayan Comprehensive Health Center

Bayanan hoto, An gina su ne domin duba marasa lafiya da ke da kananan larurori kuma ana tura masu manyan larurori asibitocin da ke birane

Kungiyoyin bayar da agaji na kasashen duniya sun fice daga kasar tun bayan da kungiyar Taliban ta karbe iko a watan Agustan da ya gabata.

Fannin lafiya na fama da matsanancin karancin magunguna da likitoci.

Ma'aikatar tsaro a karkashin Taliban ce take gaba-gaba wajen bayar da agaji ga mutanen da girgizar kasar ta aukawa kuma ta nemi agajin kasashen waje.

Ofishin bayar da agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya tura da tawagar likitoci domin bayar da agaji a yankunan da girgizar kasar ta faru.

Sannan hukumomin bayar da agaji na Pakistan da ke makwabtaka da Afghanistan su ma suna kai dauki.

Sai dai dangantakar galibin gwamnatocin kasashen waje da ta Afghanistan ta yi tsami bayan Taliban ta hambarar da gwamnatin da kasashen yammacin duniya suke mara wa baya.

Kasashe da dama sun kakaba mata takunkumai kan sha'anin bankuna kuma hakan yana tasiri sosai a harkokin tattalin arzikinta.

"Abin bakin ciki shi ne yadda aka kakaba wa gwamnati takunkumi, don haka ba ta da kudin da za ta taimaka wa mutanen da ke bukatar taimako", a cewar Abdul Qahar Balkhi, wani babban jami'i a gwamnatin Taliban.

Magunguna na dab da karewa kasancewa ba a bayar da taimakonsu da yawa ba

Asalin hoton, Gayan Comprehensive Health Center

Bayanan hoto, Magunguna na dab da karewa kasancewa ba a bayar da taimakonsu da yawa ba

Lokacin da gwamnan riko na Taliban ya je Gyan ranar Talata mutane sun yi masa ihu, suka gaya masa ya bar wurin, a cewar wani mutum a hirarsa da BBC.

Mutumin, wanda ya je domin taimaka wa mutanen da lamarin ya rutsa da su, ya ce gwamnan da kuma jami'an Taliban daga Kabul, babban birnin kasar sun yi alkawarin bayar da karin tallafi.

Tun ma kafin Taliban, asibitocin kasar a manyan birane da garuruwa, ba su da isassun kayan aikin da za su tunkari manyan bala'o'i. Kazalika babu jiragen helikwatfa na kai agaji.

A cewar jami'an lafiyar Paktika, ana fuskantar matukar karancin magungunan kashe radadi a yankin.

Yankin Gyan yana matukar bukatar tallafi daga wasu sannan  Afghanista da kasashen waje

Asalin hoton, Gayan Comprehensive Health Center

Bayanan hoto, Yankin Gyan yana matukar bukatar tallafi daga wasu sannan Afghanista da kasashen waje

Daya daga cikin likitocin da ke aiki a asibitocin wucin-gadin Gyan ya je yankin ne daga lardin Ghazni da ke da makwabtaka domin bayar da agaji.

Lokacin da ya isa yankin, mutane sun zagaye shi suna neman agaji.

Likitan ya ce ya hadu da wani matashi da ya samu karaya a kirjinsa.

Ya ce akasarin wadanda lamarin ya shafa maza da mata da kananan yara ne da aka fiddo daga baraguzan gine-gine.

Wani likita ya shaida wa BBC cewa ya hadu da kananan yara da iyayensu ba su je asibitin ba

Asalin hoton, Gayan Comprehensive Health Center

Bayanan hoto, Wani likita ya shaida wa BBC cewa ya hadu da kananan yara da iyayensu ba su je asibitin ba

An nuna wa BBC hotunan mutanen da suka samu manyan raunuka da ke jira a duba lafiyarsu.

Kazalika rahotanni sun ce an bar gawarwaki a kan tsandauri.

Masu bayar da agaji daga yankin Urgun sun isa wurin da lamarin ya faru domin kai agaji.

Wani mutum ya ce ya ga gawarwaki kusan 40 tun da sanyin safiya kuma akasarinsu na kananan yara ne.

"Ba mu samu ruwa mai tsafta ba da za mu wanke ciwukan da mutane suka ji kuma ana matukar zafi," a cewar wani likita da ya kai agaji. Wasu daga cikin mutanen da muka yi hira da su a wannan labarin ba sa so a fadi sunayensu