Newcastle ta ragargaji Man United a Premier League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Newcastle United ta ragargaji Manchester United da cin 4-1 a wasan mako na 32 a Premier League da suka buga ranar Lahadi a St James Park.

Newcastle ta fara cin ƙwallo ta hannun Sandro Tonali daga baya United ta farke ta hannun Alejandro Garnacho.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne, Newcastle ta kara biyu ta hannun Harvey Banes, sannan Bruno Guimaraes ya ci na huɗu.

Banes ya zama na biyu a Newcastle da ya ɗura ƙwallo biyu a ragar United a Premier League, bayan Alan Shearer a Disambar 2000.

Kenan Newcastle ta doke United gida da waje a Premier League a bana, bayan da ta yi nasara 2-0 a Old Trafford ranar Litinin 30 ga watan Disambar 2024.

Newcastle ta ci wasa takwas daga karawa 10 baya a wasannin gida, biyun da aka doke ta shi ne a hannun Liverpool da kuma Manchester City.

Da wannan sakamakon Newcastle ta koma ta huɗu a teburin Premier League da tazarar maki ɗaya tsakani da Man City ta biyar.

Ƙungiya biyar ce za ta wakilci Ingila a Champions League a kakar 2025/26.

Ita kuwa United tana mataki na 14 da maki 38, kwazo mai muni a Premier League, kakar da ba ta yi ƙwazo ba tun cikin karni na 1970.