Arne Slot ya ce har yanzu Jota bai murmure ba

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan gaba na Liverpool Diogo Jota zai ci gaba da jinya har sai bayan hutun wasannin ƙasa da ƙasa a watan Nuwamba saboda rauni a haƙarƙarinsa, in ji kocin ƙungiyar Arne Slot.
An cire ɗan wasan na Portugal ne a wasan da Liverpool ta doke Chelsea da ci 2-1 a ranar 20 ga watan Oktoba bayan da suka yi karo da ɗan wasan baya Tosin Adarabioyo.
Jota bai buga wasanni biyun da suka gabata ba, kuma har yanzu bai kai ga fara atisaye ba.
Ɗan wasan mai shekara 27 ba zai samu buga aƙalla wasanni huɗu masu zuwa a duk gasanni ba, inda za a yi hutun wasannin ƙasa da ƙasa daga ranar 11 zuwa 19 ga Nuwamba.
Da aka tambaye shi ko Jota zai iya dawowa kafin hutun wasannin ƙasa da ƙasa, Slot ya amsa: "A'a, sai dai bayan hutun. Elliott ma haka."
Liverpool za ta kara da Brighton, a Anfield, a gasar Premier ranar Asabar mai zuwa.
Sannan za ta karɓi baƙuncin Bayer Leverkusen a gasar cin kofin zakarun Turai inda Aston Villa za ta ziyarci Merseyside kafin a tafi hutun wasannin ƙasa da ƙasa.
Wasan farko na Liverpool bayan hutun shi ne ziyartar Southampton a ranar 24 ga Nuwamba.
Mai tsaron raga Alisson ya yi mako biyu yana jinyar rauni a cinyarsa, yayin da Elliott ke jinya ta karaya a ƙafarsa.
Chiesa, ɗan wasan da Liverpool ta ɗauko daga Juventus a bazara, ya buga wa Reds ɗin wasanni uku ne kacal a bana.











