Real na fama da masu jinya har da Vazquez da Rodrygo

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta sanar ranar Litinin cewar za ta ci gaba da wasanni ba tare da Lucas Vazquez da Rodrygo ba, sakamakon raunin da suka ji ranar Asabar.
Tun farko ƙungiyar ta sanar cewar likitoci za su yi wa Eder Militao tiyata karo na biyu a bana, bayan raunin da ya ji a wasan da Real ta doke Osasuna 4-0 a La Liga.
Militao, mai shekara 26 ɗan kasar Brazil, shi ne na biyu a Real Madrid da ya ji rauni a gwiwar kafa a bana, bayan Dani Carvajal.
Wannan dai shi ne irinsa na 10 da ɗaya daga cikin ‘yan wasan kungiyar ya samu cikin wata 15.
Cikin ƴan wasan da ke jinya a Real Madrid sun haɗa da Thibaut Courtois da Aurelien Tchouameni da kuma David Alaba.
Ana sa ran mai tsaron raga, Courtois zai koma taka leda watakila a wasan da Real Madrid za ta karɓi bakuncin Liverpool a Champions League.
Irin raunin da Militao ya ji a gwiwa ɗaya ne daga ukun da aka ci karo a La Liga a karshen mako da ya hada da na Ilias Akhomach na Villareal da kuma Enric Franquesa na Leganes.






