Tsagaita wuta a Lebanon ɗan sauƙi ne, ba mafita ga yaƙin Gabas ta Tsakiya ba

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Jeremy Bowen
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan Ƙasashen Duniya
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Yawancin mutane a Lebanon na ta murnar yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma.
Wata kwararriya kan Lebanon a wani taro kan Gabas Ta Tsakiya a birnin Rome, ta ce ta kasa yin barci lokacin da yarjejeniyar tsagaita wutar ta kusa fara aiki.
''Kamar daren jajibiren Kirsimeti ne a wajen karamin yaro. Na shiga dokin ganin batun ya fara aiki.''
Shiyasa ko'ina aka shiga annashuwa. Sama da 'yan Lebanon 3,500 ne hare-haren Isra'ila suka kashe. Mutanen da rikicin ya daidaita sun shiga cikin motocinsu da asubahi domin kokarin komawa gidajensu.
Farmakin sojin Isra'ila ya tilastawa sama da mutum miliyan daya tserewa.
An kuma jikkata dubbai da lalata gidajen dubun-dubata.
Sai dai a Isra'ila, wasu na jin cewa sun rasa damar yin babban lahani ga Hezbollah.

Asalin hoton, Reuters
Firaiminista Benjamin Netanyahu ya gana da shugabannin yankin arewacin Isra'ila, wadanda aka lalata garuruwansu zuwa kufai, inda kuma aka kwashe fararen hula kusan 60,000 zuwa kudancin kasar.
shafin yada labaran Isra'ila na Ynet ya ruwaito cewa taron ya koma na fushi da kuma yawun kalamai, inda wasu jami'ai suka fusata cewa Isra'ila na matsa lamba ga abokan gaba a Lebanon ba tare da yin wani abu na mayar da fararen hula gidajensu cikin gaggawa ba.
A wani shafin jarida, magajin garin Kiryat Shmona, kusa da kan iyaka, ya ce yana da shakku kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar, inda ya bukaci Isra'ila ta kafa wani gari a kudancin Lebanon.
A wani ra'ayin jama'a da wata tashar talbijin ta Isra'ila (Channels 12) ta gudanar, ra'ayoyi sun bambanta kan masu goyon baya da kuma wadanda ba sa goyon bayan yarjejeniyar tsagaita wuta.
Rabin wadanda aka tambaya a batun jin ra'ayin, sun yi imanin cewa ba a ci galabar Hezbollah ba kuma kashi 30 na tunanin cewa yarjejeniyar tsagaita wutar za ta rushe.

Asalin hoton, ANADOLU
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A can baya a watan Satumba, a babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya a New York, alamu sun cewa kamar an kusa cimma batun tsagaita wuta. Jami'an diflomasiyya daga Amurka da Birtaniya sun yi imanin cewa yarjejeniyar tsagita wuta na kan hanya.
Alamu sun nuna cewa dukkan bangarori da ke fada da juna sun amince da batun tsagaita wuta karkashin ka'idojin kwamitin tsaro na MDD na 1701, wadda aka zartar domin kawo karshen yakin Lebanon a shekara ta 2006: inda aka amince Hezbollah za ta janye daga kan iyaka da kuma maye gurbinsu da sojojin Lebanon. Yayin da suka fita, sojojin Isra'ila za su fice sannu a hankali.
Sai dai Firaiminista Benjamin Netanyahu ya hau kan dandali a taron na MDD tare da gabatar da jawabi cikin fushi da kuma kin amincewa da tsagaita wuta.
Komawa otel dinsa a birnin New York, mai daukar Firaiministan na Isra'ila hoto, ya dauki lokacin da ya bayar da umarnin kashe shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah, tare da wasu manyan kwamandojinsa. Daga baya ofishin Netanyahu ya fitar da hotunan, a wani abu da ake ganin kauce wa diflomasiyyar Amurka.
Kisan Nasrallah ta sake ruruta wutar rikicin da kuma janyo nakasu ga Hezbollah. Sojojin Isra'ila sun yi wa sojojin Hezbollah babban rauni tun makonnin kashe jagoran kungiyar.
Sai dai hakan bai sa kungiyar ta daina kai harin rokoki kan iyaka, inda kuma mayakanta suka cigaba da yin artabu da sojojin Isra'ila. Amma yanzu Hezbollah ba babbar barazana ba ce ga Isra'ila.
'Lokaci ne na hutawa da sake karfafa sojojinmu'
Samun nasara a bangaren soji shi ne wani abu da Benjamin Netanyahu ke tinkaho da shi, kuma lokaci ne da ya kamata a dakatar da wasu farmakin soji da ake yi da kuma sake tunani.
Shirin Isra'ila a Lebanon takaitacciya ne ba kamar Gaza ba da kuma sauran yankunan Falasdinawa da ta mamaye. Tana son korar Hezbollah ta yi nesa da iyakarta da ke arewaci da kuma barin fararen hula su koma gidajensu, musamman wadanda ke kan iyaka.
Idan Hezbollah ta yi yunkurin kai hari, Isra'ila na da amincewar Amurka na daukar matakin soji.
A wani jawabi da aka nada inda yake sanar da matakin da ya dauka, Netanyahu ya lissafa dalilai da suka janyo aka amince da tsagaita wuta a Lebanon. Ya ce Isra'ila ta girgiza Beirut, don haka lokaci ne na bai wa sojojin kasar damar sararawa da kuma sake karfafa su.
Isra'ila ta kuma karya mahadar Gaza da Lebanon. Bayan da marigayi Hassan Nasrallah ya ba da umarnin kai hari a arewacin Isra'ila, kwana guda bayan da Hamas ta kai harin na ranar 7 ga watan Oktoba, Netanyahu ya ce za su ci gaba da fada har sai an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Yanzu, Netanyahu ya ce za su kara matsa wa Hamas lamba a Gaza. Falasdinawa na fargabar sake yaduwar rikicin Gaza.
Akwai dalili daya: mayar da hankali kan abin da Netanyahu ya kira barazanar Iran. Karya lagon Hezbollah na nufin karya Iran.
Isra'ila ta ce Iran ce ta kafa kungiyar domin zamo barazana kan iyakokinta. Hezbollah ta zama babbar abokiyar Iran wajen nuna turjiya.
Me ya sa Iran ke son a tsagaita wuta
Kamar sauran jagororin Hezbollah da ke raye, manyansu a Iran ma na son a tsagaita wuta.
Hezbollah na son a tsagaita wuta domin kara daura damara. Iran na son a daina zub da jinin mambobin kungiyar. Tana ganin ganin cewa karfin kungiyar ya ragu yanzu.
Harin makami mai linzami da Iran ta kai Isra'ila bayan mutuwar Nasralla ya kara dagula al'amura.
Mutum biyu wadanda duka aka kashe yanzu, wadanda aka dauka za su sa Hezbollah ta hana Isra'ila kai hari Lebanon - su ne Qasem Soleimani, babban kwamandan Iran, wanda jirgi mara matuki na Amurka ya kashe a filin jirgin Baghdad a watan Janairun 2020.
Donald Trump ne ya bayar da umarnin a makonnin karshe na wa'adin mulkinsa na farko a fadar White House. Dayan kuma shi ne Hassan Nasrallah, wanda wani harin Isra'ila ta sama ya kashe a wajen birnin Beirut.
Hezbollah da Iran sun cigaba da zama barazana ga Isra'ila na tsawon shekara 20 bayan kawo karshen yakin 2006. Sai dai cikin sauyin da aka samu bayan harin ranar 7 ga Oktoba shi ne kin karba a takaita irin martanin da za ta mayar kan harin da aka kai mata.
Ita ma Amurka da ta kasance babbar kawarta, ba ta takaita irin makaman da take ba ta ba.
Nasrallah da Iran sun kasa ganin abin da ya faru. Ba su san ta yaya Isra'ila ta sauya ba.

Asalin hoton, Reuters












