Newcastle za ta ɗauko Kean, Ina Modric zai tafi?

Moise Kean

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Newcastle ta tattauna da wakilin ɗanwasan gaba na Fiorentina Moise Kean yayin da Arsenal da Tottenham da AC Milan da Napoli da Barcelona ke rubibin ɗanwasan mai shekara 25. (Calciomercato - in Italian)

Arsenal na shirin biyan fam miliyan 17 domin karɓo golan Espanyol Joan Garcia bayan kungiyoyi a Serie A da Bundesliga sun nuna sha'awar ɗanwasan na Spain mai shekara 23. (El Nacional - in Spanish)

Everton ta tattauna da wakilan ɗanwasan tsakiya na Freiburg mai shekara 22-Merlin Rohl. (Kicker - in German)

Real Madrid na sa ido kan ɗanwasan AC Milan da Portugal Rafael Leao, mai shekara 25 a matsayin wanda za ta iya maye gurbin ɗanwasan Brazil mai shekara 24 Vinicius Jr idan har ta yanke shawarar sayar da shi. (Fichajes - in Spanish)

Arsenal da Liverpool na hamayya kan ɗanwasan tsakiya na Crystal Palace da Ingila Eberechi Eze, mai shekara 26. (Caughtoffside)

Kocin Newcastle Eddie Howe babban mai sha'awar golan Southampton ne Aaron Ramsdale kuma yana nazarin biyan fam miliyan 25 domin ɗauko golan mai shekara 26. (Football Insider)

West Ham na shirin zubin sabbin ƴanwasa, inda za ta sayar da ƴanwasa kusan 10 a wannan bazara. (Football Insider)

Ɗanwasan tsakiya na Croatia Luka Modric, mai shekara 39, har yanzu Real Madrid ba ta nuna alamar sabunta kwangilar shi ba, inda zai iya tafiya Qatar. (Marca - in Spanish)

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ƙofarsa a buɗe take ta zama kocin Brazil a nan gaba amma idan kwangilarsa ta kawo ƙarshe a Bernabeu. (Relevo - in Spanish)

An ga tsohon kocin Manchester United Erik ten Hag a Rome kafin wasan Roma da Juventus. Dukkanin ƙungiyoyin biyu na Seria A za su shiga neman sabon koci a wannan bazara. (Radio Mana Sport Roma via Football Italia)