Jerin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su a Isra'ila

Fiye da shekara guda tun bayan da Hamas ta jagoranci hare-hare cikin Isra'ila, har yanzu akwai kusan mutum 97 da ba a san halin da suke ciki ba.
Isra'ila ta ce, Isra'ilawa 251 da 'yan ƙasashen waje aka yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Alƙaluman hukuma da Isra'ila ta fitar, sun nuna cewa har yanzu akwai mutum 101 da ke tsare a Gaza, ciki har da mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a 2014 da 2015, waɗanda aka yi imanin cewa biyu daga cikinsu sun mutu.
Ga bayanai wasu daga cikin waɗanda har yanzu ake garkuwa da su a Gaza, wanda BBC ta tabbatar ko wata majiya mai tushe.
Wannan jeri an sabunta shi, kuma sunayen ka iya sauyawa, saboda wasu mutanen da ake fargabar an yi garkuwa da su an tabbatar da cewa an kashe su ko an sake su.
An sabunta sunayen ranar 4 ga watan Disamban 2024.
Emily Damari, (mai shekara 28), mai shaidar zaman ɗan Birtaniya da Isra'ila, an kama shi daga who Kibbutz Kfar Aza.
Alexander (Sasha) Troufanov, an yi garkuwa da matashin mai shekara 28, tare da mahaifiyarsa Lena, da abokiyar zamansa Sapir Cohen, da kuma kakarsa, Irina Tati.
Dukkansu an kama su a Kibbutz Nir Oz a lokacin gudanar da bautar Sabbath tare. An saki Irina da Sapir da kuma Lenaa watan Nuwamban 2023.
Ariel Cunio, An sace Cunio, mai shekara 27, tare da abokiyar zamansa Arbel Yahud, mai shekara 29, a harin na Nir Oz.
David Cunio, mai shekara 34,ɗan'uwa ne ga Ariel, wanda shi ma aka sace shi a Nir Oz. A watan Nuwamban 2023 aka saki matsarsa Sharon Aloni Cunio da tagwayensu 'ya'yansu mata masu shekara uku Ema da Yuly.
A dai wannan watan ne aka saki 'yar uwar Sharon, Daniele Aloni, da 'yarta Emilia mai shekara shida.

Asalin hoton, Family Handout
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Doron Steinbrecher, mai shekara 31, ma'aikaciyar jinyar dabobbi, na cikin ɗakinta a Kibbutz Kfar Aza a lokacin da Hamas ta kai hari.
Naama Levy, mai shekara 20, an ɗauki bidiyonta a lokacin da ake sanya ta cikin wata motar jeef, hannuwanta ɗaure a bayan wuyanta. Hamas ce ta saki bidiyon wanda aka yaɗa sosai a shafukan sada zumunta.
Yousef Zyadna, An kama mai sana'ar sayar da madarar dabbobin, mai shekara 53, a Kibbutz Holit sannan aka tafi da shi Gaza tare da 'ya'yansa, Hamza, mai shekara 23, da Bilal, mai shekara 19, da kuma Aisha, mai shekara 17.
Ohad Ben Ami, An kama Ben Ami mai shekara 55 tare da matarsa, Raz, daga garin Be'eri, sa dai daga baya Hamas ta saki matar.
Gali da Ziv Berman An kama tagwayen masu shekara 27, daga garin Kfar Aza. Ziv na musayar saƙonni da abokinsa a lokacin da aka kai harin.
Iraq-born Shlomo Mansour, An kama dattijon mai shekara 86, a garin Kibbutz Kissufim, inda yake zaune kuma yake aiki a matsayin manajan wani gidan cin abinci.
Daniela Gilboa, matashiyar mai shekara 20, soja ce da ke aiki a Kibbutz Nahal Oz. A watan Yulin 2024 aka wallafa bidiyon mutanen da Hamas ke tsare da su, inda aka ganta a ciki tana kira ga gwamnatin Isra'ila ta taimaka ta mayar da ita da sauran mutanen gida.
Matan Angrest, matashin sojan mai shekara 21, da ke aiki da rundunar IDF, na kan aiki a ranar 7 ga watan Oktoba kuma a yanzu haka ana ƙaddarawa cewa yana Gaza.
Eli Sharabi, An kama mutumin mai shekara 52, a garin Be'eri tare da ɗan'uwansa, Yossi, wanda aka tabbatar da cewa ya mutu. A lokacin harin an kashe matar Eli tare da 'ya'yansa biyu.
Agam Berger, an yi garkuwa da matashiyar mai shekara 20, a garin Nahal Oz. An ga yadda aka sace ta cikin wani bidiyo da Hamas ta fitar a lokacin kai harin.
Edan Alexander, Mai shekara ɗan Isra'ila mai shaidar zaman Amurkan, da ya shiga aikin sojin Isra'ila bisa raɗin kansa. Ya kasance yana aiki a kusa da kan iyakar Gaza a lokacin da Hamas ta kai harin.
Matan Zanguaker, an sace matashin mai shekara 24, tare da abokiyar zamansa Ilana Gritzewsky mai shekara 31daga Nir Oz.

Asalin hoton, Family Handout
Eitan Horn, mai shekara 38, tare da ɗan'uwansa Yair mai shekara 46, 'yan asalin Argentina, na garin Nir Oz a lokacin harin.
Keith Siegel, mai shekara 65 da matarsa Adrienne - da aka fi sani da Aviva - Siegel, an sace su ne a gidansu da ke Kfar Aza. An dai saki Adrienne a watan Nuwamba.

Asalin hoton, Family Handout
Bipin Joshi, an yi amanna cewa an sace ɗalibin aikin gonar mai shekara 23, ɗan ƙasar Nepal a Kibbutz Alumim.
Oded Lifshitz, tsohon ɗan jaridar mai shekara 84, an yi garkuwa da shi a Nir Oz. Matarsa Yocheved ita ma an sace ta, kodayake an sake a cikin watan Oktoban 2023.
Omer Neutra, matashin Ba'amurken ɗan asalin Isra'ila, mai shekara 22 - wanda jika ne ga mutanen da suka tsira daga hare-haren jin jinin Yahudawa na Holocaust, na aiki a matsayin kwamanda a kusa da kan iyakar Gaza a lokacin harin Hamas. Iyayen Omer sun ce ofishin jakadancin Isra'ila cewa an yi garkuwa da shi.
Itzik Elgarat, Mai shekara 69, an ɗauke shi a Nir Oz, kuma an gano wayarsa a Gaza bayan harin.
Gadi Moses, mai shekara 80, an ɗauke shi a Nir Oz, inda yake aiki amatsayin masanin harkokin noma., an kashe abokiyar zamansa a harin, iyalansa sun ce ba asake jin ɗuriyarsa ba tun watan Disamban 2023, lokacin da ya bayyana a bidiyon farfagandar Isra'ila.
Nimrod Cohen, mai shekara 20, an ɗauke shi a Nahal Oz. Bayan kama shi mahaifinsa ya gana da Fafaroma Francis a Rome tare da wasu iyalan wadanda aka sacen.

Asalin hoton, Family Handout
Tsachi Idan, mai shekara 58 an sace shi a gidansa da ke Nahal Oz. A watan Agusta matarsa ta ce ta taɓa jin labarinsa a watan Nuwamban 2023.
Yarden Bibas, mai shekara 34, an ɗauke shi a Nir Oz tare da matarsa, Shiri da 'ya'yansu biyu, Ariel da Kfir.

Asalin hoton, Family handout
Karina Ariev, soja mai shekarua 20, na aiki a sansanin sojojin Nahal Oz lokacin da aka sace ta.
Ofer Kalderon, Hamas sun ɗauki mai shekara 53 ɗin a Nir Oz, tare da 'ya'yansa biyu, Erez da Sahar. An kashe wasu ‘yan'uwansu biyu - Carmela Dan mai shekaru 80 da jikarta Noya mai shekara 12 a harin.
Omri Miran An sace Miran mai shekara 47 daga Nahal Oz. Matarsa, Lishay, ta ce gani na ƙarshe da ta yi masa shi ne lokacin da ake kora shi zuwa cikin mota.
Liri Albag, mai shekaru 19, ya fara atisayen soji ne a matsayin jami'in tsaro a sansanin Nahal Oz lokacin da Hamas ta kai hari.
Ohad Yahalomi An yi garkuwa da mai shekaru 50 a Nir Oz, tare da dansa Eitan mai shekara 12, wanda aka sako lokacin tsagaita buɗe wuta a watan Nuwamba.
Tal Shoham, An ɗauki mai shekara 39, ne a Kibbutz Beeri. Matarsa, Adi, da ’ya’yansu biyu ƙanana, da kuma surukarsa, Dokta Shosham Haran, su ma an kama su amma an sake su a watan Nuwamba 2023.
Sagui Dekel-Chen, mai shekara 36, ɗan Isra'ila asalin Amurka an kama shi a Nir Oz.

Asalin hoton, Jonathan Dekel-Chen
Haka kuma a lokacin hare-haren an kama wasu a bikin kalankuwar kaɗe-kaɗe a kudancin Isra'ila daga cikinsu akwai:
Omer Shem Tov, mai 21, an kama shi a lokacin da yake ƙoƙarin kuɓutar da abokinsa a lokacin harin.
Yosef Ohana, mai shekara 24, ya je bikin ne tare da abokinsa.
Avinatan Or, an kama mataqshin mai shekara 31, tare da budurwarsa, oa Argamani, wadda aka sako a watan Yuni.

Asalin hoton, Family handout
Guy Gilboa-Dalal, mai shekara 23, ya halarci bikin tare da ɗan'uwansa, kuma wani mutum da aa saki ya ce an kulle su tare a ɗaki guda.
Eitan Mor, mai shekara 24, na aiki ne da jami'an da ke aikin samar da tsaro a lokacin bikin.
Alon Ohel, ɗan Sabiyan mai shekara 23, ya halarci bikin waƙoƙin a lokacin harin.
Maxim Kharkin, an gayyaci mai shekarar 36 zuwan bikin a ƙurarren lokaci, kuma sau iyu yana tura wa mahaifyarsa saƙo bayan harin.
Segev Kalfon, a lokacin da aka kai harin matashin mai shekara 26, ya ruga da guda, inda mayaƙan suka kama shi.
Romi Gonen, mai shekara 24 an yi mata kwanton ɓauna ne a lokacin da take ƙoƙarin guduwa daga wurin bikin.
Bar Kuperstein, mai shekara 23, na tsaka da aiki a wurin bikin waƙoƙin lokacin da aka kai harin.
Eliya Cohen, mai shekara 27, asn kama shi tare da budurwarsa a lokacin harin.
Elkana Bohbot, mai shekara 35, ya je wurin bikin ne tare da abokansa.
Rom Braslavski, mai shekara 20, na aiki a wurin bikin a matsayin jami'in samar da tsaro.
Omer Wenkert, manajan kula da gidan sayar da abincin mai shekara 23, an kama shia wurin bikin.

Asalin hoton, Family handout
Evyatar David, mai shekara 23, ya je wurin bikin ne tun da safe, kuma ma'aikatar wajen Isra;ila ta ce ana ci gaba da riƙe shi a Gaza.
Or Levy, da farko mai shekara 34, ya tsere daga wurin bikin tare da matarsa, amma daga bayan IDf ta ce an kashe shi ko kuma yana Gaza.
Gwamnatin Thailand ta ce an yi garkuwa da 'yan ƙasarta shida zuwa Gaza a lokacin harin.
Ta bayyana sunayensu da: Watchara Sriuan da Bannawat Seatho da Sathian Suwannakham da Nattapong Pinta da Pongsak Tanna da kuma Surasak Lamnau.
Mutanen da suka mutu daga cikin waɗanda aka yi garkuwar da su;
Akwai mutane da dama da aka yi amanna cewa sun mutu a hannun masu garkuwar. Daga cikinsu akwai:
A ranar 1 ga wata Satumba, rundunar sojan Isra'ila IDF ta bayyana cewa dakarunta sun gano gawarwakin mutum shida - Carmel Gat da Eden Yerushalmi da Hersh Goldberg-Polin da Alexander Lobanov da Almog Sarusi da Master Sgt Ori Danino. IDF ta ce Hamas ce ta kashe su jim kaɗan gabanin sojojin Isra'ila su gano inda suke.
Sai kuma a ranar 8 ga watan Agustan, kuma IDF ta bayyana cewa ta gano tare da mayar da gawarwakin Abraham Munder da Alex Dancyg da Yagev Buchshtab da Chaim Peri da Yoram Metzger da kuma Nadav Popplewell - waɗanda dukansu suka mutu a hannun masu garkuwar.
Haka ma a watan Nuwamban 2023, sojojin Isra'ila suka gano gawarwakin Noa Marciano da Yehudit Weiss mai shekara 65 a wani gini da ke kusa da asibitin Al-Shifa a birnin Gaza.
Sannan a watan Disamban 2023, sojojin na Isra'ila suka bayar da haƙuri cike da da-na-sani bayan da jami'ansu suka kashe wasu mutum uku bisa kuskure a arewacin Gaza bayan sun kuɓuta daga hannun masu garkuwar. An bayyana sunayensu da Yotam Haim mai shekara 28 da Samer Talalka shekara 22 da kuma Alon Shamriz mai shekara 26.
Bincike daga Jamie Ryan da Emma Pengelly











