Chelsea ta dawo da Chalobah mai wasannin aro a Palace

Trevor Chalobah

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Chelsea ta dawo da mai tsaron baya, Trevoh Chalobah zuwa Stamford Bridge, wanda ya buga wasannin aro a Crystal Palace.

Mai shekara 25, zai kara karfin ƙungiyar bayan da mai tsaron baya, Wesley Fofana da Benoit Badiashile ke jinya, hakan ya sa Enzo Maresca ke fuskantar kalubalen a gurbin.

Chelsea ta kira ɗan wasan ne tun daga ranar Talata a lokacin da Palace ke shirin buga Premier League da Leicester City ranar Laraba.

Sai dai wannan lamarin zai jawo cece-kuce, domin Palace ta janye mai tsaron bayan a ƙurarren lokaci, wadda ta doke Stockport County 1-0 a FA Cup ranar Lahadi.

Chalobah yana buga wasa sosai a ƙungiyar Selhurst Park, wanda ya yi karawa 14 a bana kan yarjejeniyar wasannin aro na wata huɗu da rabi.

Tun kaka ukun da ta wuce Chelsea ta yi wa Chalobah farashin £25m ga duk ƙungiyar da take bukatarsa.

Ranar Talata Chelsea ta tashi 2-2 da Bournemouth a wasan mako na 21 a Premier League a Stamford Bridge.