Ko ratse wa Mashigar Hormuz za ta magance tsadar fetur a duniya?

Duk da cewa akwai wasu hanyoyin, masana na cewa ba za su iya maye gurbin Hormuz ba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Duk da cewa akwai wasu hanyoyin, masana na cewa ba za su iya maye gurbin Hormuz ba
    • Marubuci, Luis Barrucho
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Mashigar Hormuz na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigila ta ruwa a duniya, wadda ta ƙara jan hankalin duniya musamman bayan ɓarkewar yaƙi a tsakanin Iran da Amurka.

Ƙasashen biyu sun sake komawa musayar hare-haren soji, wata guda kacal bayan sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar wucin-gadi da aka yi fatan za ta zama matakin farko na kawo ƙarshen rikicin baki ɗaya. Tuni kwance yarjejeniyar ya sa farashin ɗanyen mai ya sake tashi a kasuwannin duniya.

Amma idan jigilar ta mashigar Hormuz ta samu cikas saboda rikicin, shin akwai wasu hanyoyin da ƙasashen yankin tekun Fasha za su iya amfani da su wajen fitar da mai da iskar gas zuwa kasuwannin duniya?

Masana sun ce akwai wasu hanyoyin, amma a halin yanzu babu wata da za ta iya maye gurbin mashigar Hormuz baki ɗaya.

Me ya sa mashigar Hormuz ke da muhimmanci?

Hare-haren Iran kan jiragen dakon mai a mashigar sun sa farahin man ya tashi a kasuwannin duniya

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Hare-haren Iran kan jiragen dakon mai a mashigar sun sa farahin man ya tashi a kasuwannin duniya

Mashigar wadda ke tsakanin Iran da Oman na ɗaya daga cikin hanyoyin fitar da mafi yawan mai da iskar gas daga ƙasahe Gulf.

Hanyar ta fi sauƙi, saboda manyan tankokin mai na wucewa cikin sauƙi, kuma ya fi sauƙi kashe kuɗi idan akwa kwatanta da bututun mai, wanda ke buƙatar kula ta musamman.

A wani rahoto na hukumar makamashi ta duniya, kusan ganga miliyan 20 ne ɗanyen mai da iskar gas ke wucewa ta mashigar a kullum, wanda shi ne kimanin rubu'in adadin man fetur da ake kasuwancinsa ta ruwa, sannan kusan kashi 80 ne jiragen ruwan yankin Asia suke nufa.

Hanyoyin ratse wa Mashigar Hormuz

Map of the Arabian Peninsula titled Key pipelines that bypass the Strait of Hormuz showing major oil pipelines that bypass the Strait of Hormuz. The map highlights Saudi Arabia's East-West Pipeline, which runs across the country to the Red Sea, and the UAE's Habshan-Fujairah Pipeline, which runs to the Gulf of Oman. Nearby waterways labeled on the map include the Strait of Hormuz, the Red Sea, the Bab el-Mandeb Strait, the Indian Ocean, and the Suez Canal. Countries shown include Saudi Arabia, Iran, the UAE, Oman, and Yemen. Source: Global Energy Monitor
Bayanan hoto, Hanyoyin da za a iya ratse wa Mashigar Hormuz

Ganin yadda mahigar Hormuz ke ba Iran fifiko da ƙarfin faɗa a ji a kasuwancin makamashi a duniya ne ya sa ƙasashen Gulf suka fara zuba jari domin nemo wasu hanyoyin da za su maye gurbinta wajen fitar da albarkatun man fetur zuwa ƙasashe duniya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Babbar hanyar da aka samu ita ce ta Saudiyya, wadda ƙasar ta yi a yankin yamma maso gabashi da ake kira da Petroline mai tsawon kilomita 1,200 wadda ta haɗa matatun man ƙasar da gaɓar tekun Red Sea.

A tsakankanin shekarun 1980s aka gina a lokacin yaƙin Iran da Iraq, bayan ƙasashen sun riƙa kai hare-hare kan tankokin man fetur a tsakaninsu. Sannan a shekarar 2019 aka faɗaɗa ƙarfin bututun domin ɗaukar aƙalla ganga miliyan 7 a kullum.

Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ma ta assasa wani bututun mai mai tsawon kilomita 406 da ake kira Abu Dhabi Crude Oil Pipeline (ADCOP), wanda ke haɗa matatar Habshan ta Abu Dhabi da gaɓar Fujairah a gaɓar Oman, wanda ke ba jiragen dakon mai damar tafiya ba tare da shiga Hormuz ba.

A rahoton mujallar Financial Times, wanda ta tattauna da wasu majiyoyi, ta ce DP World, wanda kamfanin sufurin jirage ruwa ne da ke Dubai na tattaunawa domin gina katafaren filin jirgin ruwa a Fujairah.

Wannan zai sa a rage ta'allaƙa da gaɓar Jabel Ali wanda ya fi muhimmanci a Dubai, sannan zai rage rataya da Mashigar Hormuz wajen fion mai.

Sai dai duk da cewa akwai wasu hanyoyin, matsalar ita ce adadin da za su iy ɗauka. Hukumar makamashi ta duniya ta ce za su iya fitar da ganga tsakanin miliyan 3.5 zuwa miliyan 5.5 ne kawai a kullum, wanda ya yi matuƙar kaɗan idan aka kwatanta da kusan ganga miliyan 20 da ake fitarwa ta mashigar Hormuz.

"Ko kaɗan ba za su iya wadatarwa ba," in ji David B. Roberts, masanin tsaron ƙasa da ƙasa da gabas ta tsakiya a Jami'ar Kings College da ke London.

Haka kuma an sha kai farmaki kan waɗannan hanyoyin a baya. A watan Maris, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta zargi Iran da kai mata hari a matatar Fujairah, wanda dole ta dakatar da jigilar mai.

Haka kuma a watan Afrilu, an kai irin wannan harin a Petroline, wanda ya sa dole aka dakatar da loda aƙalla ganga 700,000 da ake yi a kullum, duk da kamfanin Saudi Aramco mai kula da matatar ya koma aiki bayan mako uku.

Ita ma Iran ta gina wata hanyar ratse wa mashigar Hormuz, mai nisan kilomita 1,000 daga Goreth zuwa bakin gaɓar Oman, wanda za a iya tafiyar da kusan ganga miliyan 1 a kullum zuwa kasuwannin duniya.

Ita kuma hanyar tana fama da takunkumai da suke hana ta gudanar da aiki yadda ya kamata.

Kasuwancin mai a nan gaba

Wani hoto da ke nuna hayaƙi ya turnuƙe  wani harin Amurka a kusa da mashigar Hormuz

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani hoto da ke nuna hayaƙi ya turnuƙe wani harin Amurka a kusa da mashigar Hormuz

Ana dai cigaba da tunanin samar da wasu hanyoyin da dama domin fitar da man fetur daga ƙasashen yankin Gulf ba tare da bi ta Hormuz ba.

Ɗaya daga ciki shi ne bututun Kirkuk-Ceyhan mai tsayin kilomita 600 daga yankin Kirkuk da ke arewacin Iran zuwa gaɓar Ceyha da ke Turkiyya.

An sake buɗe bututun ne a watan Satumban 2025 bayan kusan shekara biyu da rabi a rufe. Zuwa watan Maris na 2026 man da ake fitarwa ta hanyar ya kai ganga 250,000 a kullum, wanda yake matuƙar taimakon Iraq, duk da cewa ƙarami ne.

Iraq na fitar da aƙalla ganga miliyan 3.4 na ɗanyen mai ne a kullum, wanda hakan ya sa ake fitar da sauran kahi 95 ɗin ta kudancin ƙasar ta Hormuz.

Wata hanyar ita ce Kirkuk-Baniyas, wadda ke ba Iraq damar fitar da mai zuwa Syria ba tare da bi ta Gulf ba.

An kammala gina bututun mai tsayin kilomita 500 ne a shekarar 1952, amma aka fasa shi a lokacin Iran da Iraq. Amma yanzu rahotanni na nuna cewa ƙasasshen Iraqi da Syria da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa suna tattaunawa domin sake gina bututun.

Wani aikin bututun mai girma kuma shi ne na Four Seas, wanda zai haɗa tekunan Mediterranean da Black Sea da Caspian Sea da Tekun Arabia ta Syria da Turkiyya.

A watan Afrilun 2026, ministan makamashin Turkiyya Alparslan Bayraktar ne ya gabatar da buƙatar sake gyara bututun wanda aka fara maganarsa tun a 2009.

Haka kuma ana ta yekuwar a koma aikin bututun Basra-Aqaba wanda aka fara magana tun a 1983 da za a riƙa tafiyar da mai daga Iraqi ya ratsa ta Jordan, duk da cewa matsalolin siyasa da rashin kuɗi na yi wa aikin cikas.

Sai dai Huzeir Ezekiel Dzulhisham, masani a kwalejin nazarin harkokin ƙasa da ƙasa a a makarantar Singapore's S. Rajaratnam ya yi gargaɗin cewa samar da waɗannan hanyoyin za su iya barin baya da ƙura, domin a cewarsa za a iya buɗe wata ƙofar ta ta'allaƙa da wau ƙasashe daban.

Bayan Hormuz

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Hormuz

Ko da kuwa ƙasashen Gulf sun rage ta'allaƙa da mashigar Hormuz, zai yi wahala su tsira daga matsalolin da suke tattare da kasuwancin makamashi ta yankin.

Wani misalin shi ne bututun SUMED na Masar, wanda ke haɗa tekun Red Sea da Mediterranean kuma za a iya bi zuwa turai, wanda zai iya ɗaukar tsakanin ganga miliyan 2.5 zuwa miliyan 2.8.

Sai dai hare-haren maharan Houthi na kwanakin baya kan jiragen ruwa a tekun Red Sea da Bab al-Mandeb sun jefa fargaba a zukatan mutane.

Rage ta'allaƙa da Hormuz?

Dr H.A. Hellyer, masani kan harkokin gaba ta tsakiya a cibiyar masana ta Royal United Services Institute (RUSI) ya ce ƙasashen Gulf suna cigaba da ƙoƙarin samar da hanyoyin kaucewa Hormuz.

Hellyer y yi amannar cewa gwamntocin yankin za su cigaba da ƙoƙarin samar da wasu hanyoyin saboda a cewarsa ba za su rungume hannu ba.