Hukumar tace fina-finai da hisbar Kano sun samu saɓani kan masu dawulodin

Asalin hoton, Abba El-Mustapha/FB
A jihar Kano, takaddama ta kaure tsakanin hukumar Hisba da kuma hukumar Tace Fina-Finai game da sana'ar tura fina-finai wato downloading.
Tun da farko dai hukumar Hisbah ce ta fara sanar da haramta sana'ar bisa zargin cewa ana amfani da ita wajen yaɗa fina-finan batsa da sauran abubuwan da suka saɓa wa tarbiyya.
To sai dai hukumar Tace Fina-Finai ta yi fatali da wannan matakin tana mai cewa sana'ar halastacciya ce kuma ita ce ke da ikon yi ko hana sana'ar.
''Wannan mataki abu da ya kamata a ce mu da su mun zauna mun tattauna a kan makomar yin haka kasancewar mu ke da hurumi da doka ta ba mu na kula da masu wannan sana'a'', a cewar Abdullahi Sani Sulaiman kakakin hukumar.
''Akwai wani tsari da muka yi musu na rigima da suke samu tsakaninsu da masu shirya fina-finai da cewa ba za su sake ɗaukar fim ba, sai da sahalewar masu fina- finai,'' in ji shi.
A nata ɓangare, hukumar Hisba ta ce ta ɗauki matakin ne saboda ƙorafe-ƙorafe da dama da hukumar ta samu daga al'umma.
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Dakta Mujahid Aminuddeen ya shaida wa BBC cewa akwai masu fakewa da sana'ar suna tura wa jama'a hotuna da bidiyon tsiraici, lamarin da ya ce na matuƙar gurɓata tarbiya.
''Ana samun wasu ɓata-gari masu sana'ar dowulodin da ke tura wasu fina finai na batsa'', in ji shi.




