Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Utd da Arsenal da Liverpool na gogayya kan Gomes, Barca ta bi layin son Rashford
Manchester United, daArsenal, da kuma Liverpool na gogayya kan dan wasan tsakiya na Wolves Joao Gomes, dan Brazil mai shekara 23. (Sun)
Aston Villa ta kara yawan kudin tayin da ta yi wa dan gaban Borussia Dortmund Donyell Malen zuwa yuro miliyan 25 (£21m), to amma har yanzu kungiyar ta Jamus na neman yuro miliyan 30 ne a kan dan tawagar ta Netherlands mai shekara, 25. (Florian Plettenberg)
Monaco ta bi sahun kungiyoyin da suka nuna sha'awarsu ta sayen Marcus Rashford na Manchester United da Ingila. (Telegraph)
Haka ita ma Barcelona ta nuna sha'awarta ta sayen Rashford. (Fabrizio Romano)
Paris St-Germain na son dan wasan gaba mai kai hari na Aston Villa, Jhon Duran, na Colombia mai shekara 21. (RMC Sport)
Manchester United ta dage wajen ganin ta doke Tottenham a cinikin dan gaban Paris St-Germain Randal Kolo Muani, dan Faransa mai shekara 26. (Teamtalk)
Borussia Dortmund ta ayyana dan gaban Brentford Kevin Schade, na Jamus mai shekara 23 a matsayin wanda take harin saye. (Sky Sports)
Sabon kociyan West Ham Graham Potter na sha'awar sayen dan wasan tsakiya na Ingila Kiernan Dewsbury-Hall mai shekara 26, da kuma dan bayan Ingila Ben Chilwell, mai shekara 28, daga tsohuwar kungiyarsa Chelsea. (Teamtalk)
Brighton da Borussia Dortmund na son matashin dan wasan Liverpool Harvey Elliott. (Sun), mai shekara 21 wanda ke tawagar Ingila ta 'yan kasa da shekara 21.
Ipswich na duba yuwuwar sayen tsohon dan wasan tsakiya na Serbia Nemanja Matic mai shekara 36 daga Lyon. (Florian Plettenberg)
Dan wasan tsakiya na Bournemouth Philip Billing dan Denmark, ya tashi zuwa Italiya inda zai yi zaman aro Napoli
Everton na duba yuwuwar taya dan wasan gaba na gefe na Lyon, Ernest Nuamah na Ghana mai shekara 21. (RMC Sport -)
Leicester ta amince ta sayi dan bayan Parma, Woyo Coulibaly na Faransa mai shekara 25.(Gianluca di Marzio)
Fenerbahce ta tattauna da Aston Villa a kan cinikin fam miliyan 10 na dan wasanta na baya Diego Carlos na Brazil mai shekara 31.