Muna son tsawaita tazarar da muka bayar a Premier – Slot

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Arne Slot ya bayyana buƙatar ganin ƙungiyarsa ta ƙara bayar da tazara a matsayin da take a gasar Premier.

Abin da muke son ƙara ƙaimi a kai "shi ne tsawaita tazarar, domin idan ba haka ba, za ka dawo ne ka dogara da neman sa'a ko kuma rashin sa'a (na wasu) ko kuma wasu hukunce-hukunce da lafari zai yanke."

"Dole ne mu tabbatar da cewa ba ta kai inda za mu dogara da irin waɗannan abubuwa ba, kuma (tsawaita) ne abin da za mu yi idan ba mu son mu dogara kan samun sa'a ko rashin sa'a."

Liverpool na a saman tuburin gasar Premier ta Ingila da maki 46 bayan wasa 19, inda Arsenal ke biye mata da maki 40 bayan wasa 20 (tazarar maki 6).

Liverpool za ta ƙara da ƙungiyar Nottingham Forest – wadda ke matsayi na uku a kan tebur da maki 40 - ranar 14 ga watan Janairu, a wasan Premier na gaba.

Haka nan za ta kara da Brentford ranar 18 ga watan na Janairu.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da cece-ku-ce kan raɗe-raɗin yunƙurin sauya sheƙar ɗan wasan ƙungiyar ta Liverpool, Trent Alexander-Arnold zuwa Real Madrid.