Moyes na shirin komawa Everton

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

David Moyes na tattaunawa da ƙungiyar Everton a wani yunƙurinsa na sake yin kome a filin Goodison Park, bayan korar da ƙungiyar ta yi wa mai horaswa Sean Dyche.

Duk da cewa ba a cimma wata yarjejeniya ba, kuma Moyes ba shi ne kaɗai mai neman muƙamin ba, majiya mai ƙarfi ta tabbatar wa sashen wasannin motsa jiki na BBC cewa Moyes, ɗan asalin Scotland na cikin sahun gaba a batun.

Ana sa ran gudanar da tattaunawa kan kwantaraginsa a yau Juma'a.

A ranar Alhamis ne Everton – wadda yanzu haka take a matsayi na 16 a teburin Premier - ta sanar da raba gari da Dyche.

Sun yi nasara a wasa uku ne kacal cikin wasa 19 da suka buga a Premier a wannan kaka.

Moyes ya taɓa horas da Everton daga shekarar 2002 zuwa 2013, kafin ya bar ƙungiyar zuwa Manchester United.

Sai dai Moyes ya yi 'ƙarƙon-kifi' a United, inda aka sallame shi bayan wata 10 kacal.