Ɓarakar Onana ta sake sanya tababa a zukatan magoya bayan Utd

Asalin hoton, Getty Images
Mai tsaron ragar Manchester United Andre Onana ya sake ɗaukar hankali bayan da ya tafka kuskuren da ya bai wa Ipswich Town dama ta fara cin United a gasar Premier a ranar Laraba.
Kodayake a ƙarshe United ɗin ta yi nasara a wasan da ci 3-2, duk da kasancewar ta kammala wasan da mutum 10, to amma kuskuren da Onana ya yi ya sake tayar da muhawara a kan golan na Kamaru.
Onana mai shekara 28, ya yi fama a farkon zuwansa Old Trafford, amma alamu suka nuna ya fara sabawa da yanayin wasan ƙungiyar a farkon kakar nan, lokacin da ya zama mai tsaron ragar da ya fi kowanne nasarar kare ragarsa a gasar ta Premier da ƙwallo shida kawai aka ɗaga ragarsa.
Sai dai katoɓarar da ya yi minti huɗu da fara wasa ranar Laraba da Ipswich, ta sake nuna dalilin da ya sa magoya bayan ƙungiyar da kuma masu sharhi ke nuna tababa a kan cancantarsa a ƙungiyar.
United ta sayi golan a kan fam miliyan 47 daga Inter Milan a kakar 2023 domin maye gurbin gwarzon ɗanwasan ƙungiyar na shekara huɗu a jere, mai tsaron raga David de Gea.
To amma duk da burin da ƙungiyar ke da shi a kansa da kuma ƙwarin gwiwar cewa zai iya tsare mata raga kamar wanda ya gada ko ma ya fi shi, ya gaza tadda De Gean ballantana ma ya zarta shi idan aka dubu alƙaluman bajintarsu.
Onana ya tafka kura-kurai na inna-naha a gasar Zakarun Turai a bara, da hakan ya sa aka yi waje da ƙungiyar da wuri tun ma a matakin wasannin rukuni.
Kuma a yanzu ma tuni ya sake tafka wasu kura-kuran a wasansu da Viktoria Plzen, da Brighton da kuma Nottingham Forest a kakar nan kafin ma katoɓarar da ya yi a wasan Ipswich, yayin da ya koma baya a jerin masu tsaron ragar da ake ganin za su ciri tuta a kakar bana da kyautar bajinta ta Golden Glove.












