Champions League: Arsenal da Barca sun kai kwata fainals

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe, bayan da ta yi nasara a kan FC Porto da cin 4-2 a bugun fenariti ranar Talata a Emirates.
Tun farko Arsenal ce ta ci 1-0 ta hannun Leandro Trossard saura minti hutu su je hutu - irin wannan sakamakon Porto ta samu a Portugal a wasan farko.
Hakan ne ya sa aka yi karin lokaci daga nan aka je bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Gunners ta ci kwallaye a bugun fenariri ta hannun Odegaard da Kai Havertz da Bukayo Saka da kuma Declan Rice.
Mai tsaron ragar Arsenal, David Raya ya tare kwallon da Wendell da na Galeno da suka buga masa.
Da wannan sakamakon Gunners ta kai kwata fainals a Champions League a karon farko tun 2009/10.
Haka kuma Gunners ta kawo karshen rashin nasara bakwai a jere a zagayen 'yan 16 a gasar ta zakarun Turai.
Leandro Trossard ya zama na uku da ya ci kwallo a wasa uku a Champions League a gidan Arsenal, bayan Alexis Sánchez da kuma Bukayo Saka.
Martin Odegaard ya bayar da kwallo bakwai aka zura a raga a bana a dukkan fafatawa har da daya a Champions League.
Mai tsaron bayan Porto, Pepe ya zama na farko da ya buga Champions League yana da shekara 41.
Wasan Champions League tsakanin Arsenal da FC Porto

Asalin hoton, Getty Images
2023/2024
Champions League Talata 12 ga watan Maris din 2024
- Arsenal 1 - 0 Porto
Champions League Laraba 21 ga watan Fabrairun 2024
- Porto 1 - 0 Arsenal
2009/2010
Champions League Talata 9 ga watan Maris din 2010
- Arsenal 5 - 0 Porto
Champions League Laraba 17 ga watan Fabrairun 2010
- Porto 2 - 1 Arsenal
2008/2009
Champions League Laraba 10 ga watan Disambar 2008
- Porto 2 - 0 Arsenal
Champions League Tu 30Sep 2008
- Arsenal 4 - 0 Porto
2006/2007
Champions League We 06Dec 2006
- Porto 0 - 0 Arsenal
Champions League Tu 26Sep 2006
- Arsenal 2 - 0 Porto

Asalin hoton, Reuters
Barcelona ta kai kwata fainals a Champions League, bayan da ta doke Napoli 3-1 a Sifaniya ranar Talata.
Barcelona ta kai zagayen gaba da cin kwallo 4-2 kenan gida da waje, bayan da suka tashi 1-1 a wasan farko a Italiya.
Barcelona ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe a Champions League a karon farko tun bayan 2019/20.
A kuma lokacin kungiyar Sifaniya ta yi nasara da cin kwallo 4-2 gida da waje a kan Napoli.
An yi waje da Napoli a Champions League a irin wannan mataki karo hudu daga fafatawa biyar - haka kuma kungiyar Italiya ta yi rashin nasara a wasa biyar daga shida a zagayen ziri daya kwale.
Sakamakon wasa tsakanin Barcelona da Napoli

Asalin hoton, Reuters
2023/2024
Champions League Talata 12 ga watan Maris din 2024
Barcelona 3 - 1 Napoli
Champions League Laraba 21 ga watan Fabrairun 2024
- Napoli 1 - 1 Barcelona
2021/2022
Europa League Alhamis 24 ga watan Fabrairun 2022
- Napoli 2 - 4 Barcelona
Europa League Alhamis 17 ga watan Fabrairun 2022
- Barcelona 1 - 1 Napoli
2019/2020
Champions League Asabar 08 ga watan Agustan 2020
- Barcelona 3 - 1 Napoli
Champions League Talata 25 ga watan Fabrairun 2020
- Napoli 1 - 1 Barcelona
Wadanda suka kai zagayen daf da na kusa da na karshe
Barcelona (Spain)
Bayern Munich (Jamus)
Manchester City (Ingila)
Paris St-Germain (France)
Real Madrid (Spain)
Arsenal (Ingila)
Wasannin da za a buga ranar Laraba:
- Atletico Madrid da Inter Milan
- Borussia Dortmund da SV Eindhoven











