Ancelotti ya ja ragamar Real Madrid wasa na 179 ya haura Mourinho

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta je ta doke Espanyol da ci 3-1 a wasan mako na uku a gasar La Liga da suka fafata ranar Lahadi.
Minti na 12 da fara wasan Vinicius Junior ya ci wa Real kwallo, sauran minti biyu su je hutu ne Espanyol ta farke ta hannun Joselu.
Sauran minti biyu a tashi daga wasan Real ta kara na biyu ta hannun Karim Benzema, sannan ya ci na uku na biyu a wasan daf da za a tashi.
Wasa na 179 da koci Carlo Ancelotti ya ja ragamar Real Madrid kenan ya kuma hau kan Jose Mourinho a jerin wadanda suka ja kungiyar wasanni da dama.
Cikin wadan nan wasannin Ancelotti ya ci karawa 132 da canjaras 22 da rashin nasara 25.
Kenan dan kasar Italiya shi ne na shida a jerin wadanda suka ja ragamar Real wasanni da yawa, ya haura Mourinho mai 178.
Wadanda ke gaban Ancelotti sun hada da Miguel Munoz mai wasa 605 da Zidane da ya ja ragamar karawa 263 da Del Bosque mai 246 da Beenhakker 197 da kuma Molowny da ya ja ragamar wasannin Real karawa 183.
Cikin wasa 179 da Ancelotti ya ja ragama sun hada da 117 a La Liga da 38 a Champions League da 16 a Copa del Rey da hudu a Spanish Super Cup da wasa biyu a Club World Cup da kuma biyu a European Super Cup.
A matakinsa na kociyan Real Madrid ya lashe kofi takwas a kungiyar da suka hada da Champions League biyu da Club World Cup daya da European Super Cups biyu da LaLiga daya da Copa del Rey daya da kuma Spanish Super Cup daya.

Asalin hoton, Getty Images









