'Yan wasan Real Madrid da suka je Villareal buga Copa del Rey

Real Madrid

Asalin hoton, Real Madrid FC

An wallafa

Real Madrid ta ziyarci Villareal, domin buga Copa del Rey wasan zagaye 'yan 16 da za su kara ranar Alhamis a Estadio de La Ceramica.

Ranar 7 ga watan Janairun 2023 Villareal ta doke Real Madrid a wasan La Liga da ci 2-1.

Real Madrid mai maki 38 tana ta biyu a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki uku tsakaninta da Barcelona mai maki 41 ta daya.

Ita kuwa Villareal tana ta hudu a teburin La Liga mai maki 28, wato da tazarar 10 tsakaninta da Real Madrid.

Real wadda ta lashe European Super Cup a bana ta sha kashi a hannun Barcelona da ci 3-1 a Spanish Super Cup a Saudia Arabia ranar 15 ga watan Janairu.

Real ce ke rike da Spanish Cup na bara na 12 jumulla, wanda Barcelona ta karbe a bana ta hada na 14 a tarihi.

Real wadda za ta buga Club World Cup a Morocco cikin watan Fabrairu, za ta ziyarci Athletic Bilbao ranar 22 ga watan janairu a gasar La Liga.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da Luis Lopez.

Masu tsaron baya: E. Militão, Vallejo, Nacho, Odriozola, Rüdiger, F. Mendy da Tobias.

Masu wasan tsakiya: Kroos, Camavinga, Valverde, D. Ceballos da Mario Martín.

Masu cin kwallo: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da Mariano.