Argentina ta dare matakin farko a Fifa ta yi kasa da Brazil

Argentina

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Argentina ta koma ta daya a kan jadawalin kasashen da ke kan gaba a taka leda a duniya da Fifa ta sanar.

Karon farko da Argentina ta hau kan wannan matakin tun bayan shekara shida, wadda ta lashe kofin duniya a Qatar a 2022.

Argentina ta samu wanan ci gaban bayan nasara biyu a wasan sada zumunta da ta ci Panama da Curacao, ita kuwa Brazil rashin nasara ta yi a hannun Morocco.

Faransa, wadda ta doke Netherlands da Jamhuriyar Ireland a wasannin neman shiga Euro 2024 ta koma ta biyu.

Brazil wadda take matakin farko ta koma ta uku, Ingila wadda ta ci Italiya da Ukraine tana ta biyar da Sifaniya a jerin 'yan 10 farko.

Jerin goman farko a Fifa

1 Argentina Argentina

2 France

3 Brazil

4 Belgium

5 England

6 Netherlands

7 Croatia

8 Italy

9 Portugal

10 Spain

Super Eagles wadda Jose Pesseiro ke jan ragama ta yi kasa ajadawlin kungiyoyin da ke kan gaba a taka leda a duniya.

Super Eagles

Asalin hoton, Super Eagles

Najeriya wadda ta je ta ci Guinea Bissau 1-0 a watan jiya a wasan cikin rukuni a neman shiga kofin Afirka tana ta 40 a duniya, wadda take ta 35 a Disamba.

A nahiyar Afirka kuwa Super Eagles wadda take ta biyar a baya yanzu Masar ta karbi gurbin, Najeriya ta yi kasa zuwa ta shida.

Itama Kamaru ta yi kasa daga mataki na hudu a baya yanzu tana ta bakwai a Afirka.

Jerin 10 farnfo a tamaula a Afirka

  • Morocco
  • Senegal
  • Tunisia
  • Algeria
  • Masar
  • Najeriya
  • Kamaru
  • Ivory Coast
  • Burkina Faso
  • Mali