An yi hutu a La Liga Barcelona tana jan ragamar teburi

Asalin hoton, Getty Images
Za a ci gaba da wasannin La Liga a karshen watan Disambar 2022, bayan da aka kammala karawar mako na 14 ranar 10 ga watan Nuwamba.
Tun daga lokacin aka fara hutun buga gasar cin kofin duniya da za a fara a Qatar daga 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022.
Za a koma gasar La Liga ranar Asabar 31 ga watan Disambar 2022, bayan da aka yi hutu Barcelona na jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Kawo yanzu saura karawa 24 a kammala gasar La Liga, Barcelona tana matakin farko da maki 37.
Kungiyar Nou Camp ta yi nasara a wasa 12 da canjaras daya da rashin nasara a karawa daya da cin kwallo 35 aka zura mata biyar a raga.
Cikin kungiyoyin da Barca ta ci har da Cadiz da Elche da Real Mallorca da Celta de Vigo da Villareal da Atletico Bilbao da Valencia da Almeria da kuma Osasuna.
To sai dai kungiyar da Xavi ke jan ragama ta yi rashin nasara a hannun Real Madrid a kakar nan.
Real Madrid mai rike da kofin bara tana ta biyu da tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona ta kuma yi nasara a wasa 11 da canjaras daya aka doke ta a daya.
Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama ta zura kwallo 33 a raga, ita kuma an zura mata 14.
Za a ci gaba da wasannin mako na 15 a gasar La Liga ranar Asabar 31 ga watan Disamba, Barcelona za ta fafata da Espanyol, inda Real Madrid za ta ziyarci Real Valladolid.
Za a koma La Liga ranar Asabar 31 ga watan Disambar 2022
- Atletico Madrid da Elche
- FC Barcelona da Espanyol
- Real Betis da Athletic de Bilbao
- Celta de Vigo da Sevilla
- Real Sociedad da Osasuna
- Real Valladolid da Real Madrid CF
- Villarreal da Valencia
- Getafe da Real Mallorca
- Cadiz da UD Almeria
- Girona da Rayo Vallecano
Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a La Liga:

Asalin hoton, Getty Images
- Robert Lewandowski Barcelona 13
- Vedat Muriqi Real Mallorca 8
- Borja Iglesias Real Betis 8
- Joselu Espanyol 7
- Iago Aspas Celta de Vigo 7
- Vinicius Junior Real Madrid 6
- Federico Valverde Real Madrid 6
- Ezequiel Avila Osasuna. 6
- Brais Mendez Real Sociedad 6
- Antoine Griezmann Atletico Madrid 5
- Gorka Guruzeta Athletic Bilbao 5
- Alvaro Morata Atletico Madrid 5
- Inaki Williams Athletic Bilbao 5
- Karim Benzema Real Madrid 5
- Sergio Leon Real Valladolid 5









