An ci wasa na 100 da Rodrygo a Real Madrid ranar Asabar

Rodrygo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ranar Asabar Real Madrid ta je ta doke Real Sociedad 2-0 a wasan mako na biyar a La Liga da suka kara a Reale Arena.

Wasa na 100 da Real Madrid ta lashe tare da ɗan wasan Brazil, Rodrygo a karawar da ya buga mata a La Liga.

Kawo yanzu ya yi mata wwasa 147 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da cin ƙwallo 27, wanda ya lashe kofin La Liga uku a 2020 da 2022 da kuma 2024.

Rodrygo yana kaka ta shida a Santiago Bernabeu, shekarar da ya fi taka rawar gani ita ce a bara, wadda aka ci wasa 25 da shi da ta 2021/22 da Real ta yi nasara 21.

Ƙungiyar Athletic Club, ita ce wadda Real Madrid ta doke karo bakwai tare da Rodrygo.

Real Madrid ta haɗa maki 11, bayan cin wasa uku a La Liga da yin canjaras biyu da fara kakar nan.

Ranar Talata, Real Madrid za ta karɓi bakuncin Stuttgard a wasan farko a cikin rukuni a Champions League, wato 17 ga watan Satumba.

Daga nan kuma Espanyol za ta je gidan Real Madrid a wasan mako na shida a La Liga ranar Asabar 221 ga watan Satumba.