Mece ce cutar olsa, kuma mene ne haƙiƙanin abin da ke jawo ta?

Hoton mutum ya danne cikinsa

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

A duk lokacin da mutum ya ji cikinsa ya ɗauki zafi ko yana rugugi, a lokuta da dama tunanin da yake zuwa masa shi ne ko dai yana da cutar ulcer ne, lamarin da masana suka ce ko kusa ba haka yake ba.

Ulcer cuta ce da ta daɗe tana yi wa mutane illa, inda take hargitsa mutane, har idan ta yi muni, mutane sukan riƙa yin aman jini.

Wani abu da ya daɗe a bakin mutane shi ne rashin cin abinci, ko jinkirin cin abincin ne kan gaba wajen jawo cutar, lamarin da masana kiwon lafiya suka musanta.

Haka kuma tun shekaru aru-aru, da zarar an ji alamar ulcer, akan buƙaci mutum ya sha madara domin samun sauƙi, wanda hakan ya sa ake tunanin madara tana maganin cutar ko rage raɗaɗinta.

Hakan ya sa cutar ke ɗauke da ruɗani da ɗaure kai kan abubuwan da suke sabbaba ta, da kuma haƙiƙanin maganinta.

Mece ce cutar ulcer ɗin?

Ganin ana samun saɓanin fahimta kan ainahin asalin cutar ta ulcer, BBC ta tuntuɓi Dakta Yusuf Musa, ƙwararren likitan abubuwan da suka shafi ciki wato Gastrointestinal Hypologist da ke Asibitin Koyarwa da ke Katsina.

Dr Yusuf ya ce ulcer gyambon ciki ne, "Duk da dai gyambon ba a cikin baki ɗaya yake ba, ko dai a maƙoshi ko a tumbi ko a ƙaramin hanji. Nan ne ake samun gyambon."

Amma ya ce akwai abubuwan da suke jawo mutane kan ji zafin ciki bayan cutar ta ulcer.

"Amma shi ulcer shi ne a samu wani wuri ko dai maƙoshi ko tumbin ko kuma a cikin ƙaramin hanji ya buɗe ko ya ƙwarzane, sai ya zama ciwo," in ji shi.

Ya ce kamar yadda ciwo a waje yake warkewa, haka nan ciwo ma a cikin ma yana warkewa, "sai dai idan ba a yi abin da ya dace ba."

Me ke jawo cutar?

Ulcer

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Yusf ya ce akwai abubuwan da bincike ya tabbatar suna jawo cutar ulcer da rugugi ko zafin ciki.

  • Helicobacter pylori: Wata ƙwayar cuta ce da aka tabbatar tana jawo cutar kuma tana yawo sosai a cikin al'umma, musamman a ƙananan ƙasashe.
  • Shan maganin ciwon jiki: Akwai magungunan ciwon jiki daban-daban da shansu yana jawo cutar.
  • Magungunan gargajiya; Su irin waɗannan magungunan yawanci ba a san abubuwan da ke ke ƙunshe a ciki ba.
  • 'Stress ulcer': Shi ne ake samu idan mutum ya yi haɗarin mota, sai ya ji ciwon ko ya ƙone.

Sai dai ya ce yawancin abubuwan da mutane suke alaƙantawa da suna jawo cutar, kamar yaji ko yunwa, ba haka ba ne, domin a cewarsa, "babu wata tabbatacciyar alaƙa tsakanin waɗannan abubuwa da cutar."

Sai ya ce "ba ka iya sanin kana da ulcer ɗin ko ba ka da ita sai an je asibiti. Da yawan mutane kawai suna jin abin da suke ji ne a ciki, sai su ce suna da ulcer, alhali yawanci ba ita ba ce."

Shin madara na magance cutar?

A tsawon zamanunnuka, idan mutum ya fara jin rugugi ko zafin ciki, a kan ce ya sha madara, inda mutane da dama suka yi amannar tana maganin culer.

Sai dai likitan ya ce, "Game da abubuwan da suka shafi ulcer akwai abubuwa da muke ake kira 'myth', wato shashi-faɗi ne kawai. Daga ciki akwai maganar shan madara."

Ya ce madara ba maganin ulcer ba ce, "akwai na'ukan matsalolin da suka shafi zafin ciki waɗanda ba dole sai ita ulcer ɗin ba, daga cikin abubuwan da muke ba su shawara su rage amfani da su, akwai madara da lemuka waɗanda da ake kira carbonated drinks. Don haka a iya sanina madara ba maganin ulcer ba ce."

Ya ce ba kowane zafin ciki ba ne ulcer, sannan a cewarsa masu ganin zafin cikin ya ragu bayan sun sha madara, "kawai abin da ake 'psychological belief' wato yarda ce kawai. Kamar wanda ka ba wani ruwa ne a matsayin maganin wani abu, idan ka sha sai ka samu sauƙi. Ba maganin ba ne, yarda ce kawai."

Kira ga masu jin zafin ciki

A game da abin da ya kamata mutum ya yi idan ya ji zafin ciki, Dakta Yusuf ya ce kasancewar ba kowane rugugin ciki ba ne ke alamta cutar ulcer, inda a cewarsa, "Abin da ya kamata shi ne idan ka ji wata damuwa abu mafi kyau shi ne ka je asibiti. Idan ma likitan da kake zuwa wajensa ba ƙwararre ba ne, ka je ka ga ƙwararren likitan fannin, za a samu waraka.

Ya ce akwai bambanci tsakanin iri-irin zafin ciki, inda ya ce da wahala a gane bambanci, "Idan mutum ya je asibiti ne za a yi masa tambayoyi, a tantance shi. Daga waɗannan bayanan ne za a gane yana da ulcer ne ko wani abun ne dabam."