Ko Ukraine za ta iya jure ƙarin shekara ɗaya na yaƙi?

Sojojin Ukraine biyu suna ƙarbar horo kan amfani da makami
    • Marubuci, Jonathan Beale
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Defence Correspondent
    • Aiko rahoto daga, Dnipro
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Ukraine na rashin nasara a yaƙin da take yi. Sojojinta da dama sun fara gajiyawa bayan shafe shekara uku suna yaƙi.

Tambayar a nan ita ce ƙo ƙasar za ta iya jure ƙarin shekara ɗaya na yaƙi?

Dakarunsu na cigaba da ƙoƙarin daƙile kusantowar sojin Rasha a gabashi.

Sai dai sun kusan ƙewaye su a kusa da garin Kurakhove- wurin da ake ta gwabza mummunan yaƙi a maƙonnin da suka gabata.

Wani rukunin dakarun masu amfani da makamin mortar mai suna 'The Black Pack' na ƙoƙarin kare kewayesu da ake ƙoƙarin yi a Kurakhove.

Sojin Rasha na ƙara kusantowa daga ɓangarori uku.

Mun haɗu da tawagar rukunin a wani ɓoyayyen gida suna hutawa bayan yaƙin.

Ba sojojin da aka saba gani ba ne. Sun haɗa da mai dafa abinci, bakanike, mai samar da shafin intanet da kuma mai zane. Duk sun sa kansu za suyi yaƙin.

Surt, kwamandansu mai shekara 31, ya shiga cikin sojin jim kaɗan bayan mamayar Rasha.

Ya shaida min a farko ya yi tunanin yaƙin zai ƙare bayan shekara uku.

Amma yanzu, a cewarsa, yana shirya kansa kan ƙarin shekara 10 ana yaƙi.

Surt, kwamanda mai shekara 31, ya ɓoye fuskarsa.
Bayanan hoto, Surt says he worries about the outcome of any future negotiations
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dukkaninsu sun san cewa Donald Trump na ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da shugaban Rasha sun nuna alamar cewa a shirye suke su tattauna, sai dai tunanin samun yarjejeniyar da za ta dace ga kowa abu ne da ake ganin mai wuya.

Zuwa yanzu dai, maganganu kawai ake ta yi a kan wasu maganganun.

Surt bai yi watsi da burin Trump ba.

''Shi mutum ne mai buruka, kuma ina ganin zai yi ƙoƙarin yin haka,'' a cewar sa.

Sai dai ya nuna damuwa kan sakamakon duk wata tattaunawar zaman lafiya.

''Mu mutane ne da muka san abin da zai yiwu da wanda ba zai yiwu ba, mun fahimci cewa ba za a yi adalci ga Ukraine ba- dole wasu su yi haƙuri su amince da cewa rokoki sun lalata gidajensu, da kuma cewa an kashe masoyansu, kuma wannan abu ne mai wahala.''

Da na tambayeshi ko ya fi son a yi tattaunawar zaman lafiya ko kuma a cigaba da yaƙi- Surt ya amsa min cewa: '' a cigaba da yaƙi.''

Wannan mahanga ce ta akasarin waɗanda ke rukunin. Serhiy, ya yi imanin cewa tattaunawa zai tsayar da yaƙin ne na wucin-gadi- '' kuma yaƙin zai cigaba cikin shekara ɗaya ko biyu.''

Ya yarda cewa yanayin da ake ciki a yanzu ba yanayi mai kyau ba ne ga Ukraine.

Sai dai shi ma a shirye yake ya cigaba da yaƙin. Kashe shi, a cewar sa, '' ɗaya ne kawai daga cikin bala'oin mamaya.''

Davyd wanda shi ma soja ne, ya na tsaye a cikin ɓoyayyen gidansu.
Bayanan hoto, Davyd, an artist and soldier

Davyd, mai zanen, a ganinsa, Trump mutum ne da ba za a iya hasashe kan abin da zai yi ba, kuma hakan abun damuwa ne. '' Zai iya kasancewa alkhairi ko rashin alkhairi ga Ukraine,'' inji shi.

Rukunin na shafe mako guda a fagen yaƙi sai mako na gaba kuma su na hutawa. Sai dai duk da suna hutu, su na cigaba da karɓan horo, saboda a cewar su yana ƙara musu ƙaimi.

A cikin yanayi na sanyi, su na ƙarbar horo kan yadda zasuyi amfani da makamansu.

A kwanakin baya, Denys, wanda ya baro gidansa da ke Jamus, ya shiga cikin tawagar.

''Na yi wa kaina wannan tambayar- shin zan iya rayuwa a duniyar da babu Ukraine a cikinta?'' a cewar sa. Ba a son ran sa ba, ya amince cewa alamu sun nuna a yanzu a na rashin nasara, sai dai ya ƙara da cewa: '' idan ba ku gwada yin nasara ba, to tabbas ne zakuyi rashin nasara. Akalla zan mutu ina ƙoƙarin samun nasara.''

Sai dai ba kaman sauran ba, Denys ya ce yakamata a ce aƙalla Ukraine ta yi la'akari da batun tsagaita wuta.

Yana ganin waɗanda yaƙin ya rutsa da su a Ukraine sun fi adadin da aka amince, wato mutane 400,000 da aka ce an kashe da kuma hallaka.

'' Kawai ina ganin dayawa daga cikin jajirtattun sojojin ko dai sun ɓace ko kuma sun gaji matuƙa, kuma a gani na ba wai muna son a tsagaita wuta ba ne, sai dai ba za mu iya cigaba da yaƙi na tsawon wasu shekaru nan gaba ba'' inji shi.

Denys na tsaye a waje sanye da kayan sojoji
Bayanan hoto, Denys voluntarily joined from Germany

Dnipro, birni na uku mafi girma a Ukraine na nuna alamar ƙin amincewa da cigaba da yaƙin da aka shafe shekaru ana yi.

Wuri ne da ake kai hare haren makamai masu linzami da kuma jirage maras matuƙa a lokuta da dama.

Ana jiyo ƙarar alamar gargadin hari daga sama a safiya da kuma dare.

A lokacin da ba a jin ƙarar, ƴan Ukraine na ƙoƙarin yin rayuwar su ta yau da kullun kamar a baya, a wannan lokaci da komai ya sauya- ciki har da zuwa gidajen wasan kwaikwayo.

A wani wasan kwaikwayo na barkwanci wanda a ke kira Iyalan Kaidash, duk da haka ana samun abubuwan da ke sa a tuna yaƙin kamar yin shiru na minti ɗaya domin tuna sojojin da suka mutu da kuma yin taken Ukraine.

Sai dai wasu daga cikin masu kallo sun yarda cewa su na fatan samun maslaha mai ɗorewa.

Ludmyla ta ce min '' abin taƙaici shi ne kaɗan daga cikin mu ne suka rage. Muna samun taimako, amma ba ya isa- shiyasa ya kamata mu zauna mu tattauna,''

Ita kuwa Kseniia cewa ta ke: '' Babu amsa mai sauƙi. An kashe sojojin mu da dama. Sunyi yaƙi saboda wani abu- wato ƙasar mu. Amma ina so yaƙin ya zo ƙarshe.''

Ƙuri'un jin ra'ayoyin jama'a ma na nuna ana cigaba da samun karuwar goyon bayan tattaunawar zaman lafiya.

Wata mata a kan dandamali a lokacin wasan kwaikwayo a Dnipro.
Bayanan hoto, The show must go on in Dnipro

Wasu daga cikin manyan kiraye kirayen da ake yi na tsagaita wuta na zuwa ne daga waɗanda aka tilastawa tserewa saboda yaƙin.

A wata mafaka kusa da gidan wasan ƙwaiƙwayon, a wani tsohon gidan da ɗalibai ke zama, wasu tsoffafin mata hudu suna tuna baya kan gidajensu da suka baro.

Valentyna ƴar shekara tamanin da bakwai ta ce ta zo wurin ba tare da komai ba, amma an samar mata da talakma, kaya da kuma abinci.

Ta ce ana kula da su sosai. ''yanada daɗi ka zama baƙo, amma ya fi daɗi ka zama kana gidanka.''

Valentyna da Mariia, tsofaffin mata biyu da suka rasa muhalansu a cikin gidansu na wucin gadi.
Bayanan hoto, Valentyna da Mariia sun bar gidanjensu da a yanzu yake yankin da Rasha ke da iko.

Yanzu gidanta na yankin da Rasha ta mamaye. Dukkanin matan huɗu suna son ayi tattaunawar zaman lafiya.

Sai dai Mariia, mai shekaru 89, ta ce bata san yadda ''ɓangarorin biyu za su kalli cikin kwayar idon juna ba, bayan ta'asar da dukkansu sukayi.''

Ta kara da cewa: '' a bayyane yake babu wanda zaiyi nasara ta hanyar amfani da sojoji, hakan yasa mu ke buƙatar tattaunawar zaman lafiya.''

Idan aka yi tattaunawar zaman lafiya, a ƙarshe waɗannan matan ne za suyi sadaukarwar da tafi ta kowa- ganin cewa akwai yiwuwar Ukarine za ta sadaukar da filin ƙasa domin zaman lafiya.

Ƙarin rahoto daga Daniel Wittenberg da kuma Anastasiia Levchenko.