Yadda batun kayyade shekarun masu son takarar shugaban Najeriya ya fara tayar da kura

.

Asalin hoton, BENJAMIN KALU

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Jam'iyyun adawa a Najeriya sun fara nuna adawarsu kan wani matakin da 'yan majalisar wakilan kasar suka dauka da zai kayyade shekarun 'yan takarar da za su tsaya neman mukamin shugaban kasa da gwamna da cewa kada su zarce sittin.

Kudurin dokar ya tsallake karatu na farko da na biyu, wanda hakan ke nufin ya na daf da zama doka.

ldan kudurin ya samu sahalewar yan majalisar Najeriyar har ya kai ga zama doka, zai hana mutane da dama tsayawa neman takarar shugabancin kasar.

Manyan jami'yyun hamayya a Najeriyar sun zargin 'yan majalisa da barin abinda ya fi muhimmanci, kamar yaki da cin hanci da rashawa, da kyautata rayuwar yan kasar ne ya fi mahimmanci, ba wai maganar yawan shekaru ba.

Jam'iyyar PDP wadda ta soki wannan yunkuri, ta bayyana shi da abin nan da hausa ke cewar saki reshe ne kama ganye.

lbrahim Abdullahi shi ne mataimakin sakataren yada labaran jam'iyyar ta PDP a Najeriya ya ce kudurin bashi da maraba da take yancin 'yan kasa, wanda ko kadan basa maraba da shi.

"Sau da yawa mun ga yadda matsa suka rike mulki babu wani alkahiri da ya biyo baya haka su ma dattawan suma munga haka, a wani banagren kuma mun ga matasan da dattawan da su ma suka taka rawar azo a gani.

Saboda haka nasarar dimokaradiyya baya tatatare da shekarun ‚yan takara ko shuwagabanin, illa iya ka ana son mutum da ya san ya kamata, wanda ya kware a tafi da mulki, saboda yunkurin yan majalisar ba abu ne da yan kasa ke bukatar sa ba a yanzu, don haka mu bama tare da shi," In ji Ibahim Abdullahi.

Ita ma jam'iyyar Labour, ta ce akwai sake kann wannan wannan kudurin doka.

Dakta Tanko Yunusa mai magana da yawun jam'iyyar ya ce 'Anan yin san e a yanzu don a daukaka dimokaradiyyar mu, ko kuwa ana so a yiwa wasu bita da kulli, don kaga mu muna goyan bayan Peter Obi, Peter Obi kuwa ya haura shekaru 60, kaga kenan zangon kasa ake so aa dankile masa bukatar sa na neman takara shugabancin Najeriya, wanda kuma ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya, da ke cewar kowa na da dama da yancin neman kowacce kujera muddin shi dan kasa ne,' in ji dr Tankon.

Martanin yan majalisar

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hon Alasan Ado Doguwa Daya ne daga cikin yan majalisar wakilan ta Najeriya da ke wakiltar mazabar Tudun wada da Doguwa a majalisar, ya ce wannan bukata ce da wasu yan majalisa suka gabatar, kuma kuduri zai yi wahala ya samu karbuwaa wajen takwarorinsu.

"Ba wai wani shiri ne ko wani kuduri na musamman ba da majalisa ta ke yi don yi wa shekarun masu tsayawa takarar shugaban kasa gyara ba, a'a wani dan majalisa ne ya gabatar da kudurin, wanda ya sami karatu na farko da na biyu, amma abin da na ke son mutane su fahimta shi ne, idan ka ce za ka yi wa wannan doka gyara na cewar wanda ya kai shekaru 60 tsayawa takarar ba, to akwai wadan da baza a yi musu adalci ba", a cewar Doguwa.

Idan wannan kuduri va zama doka to shugaban kasa be Ahmed Tinubu da tsohon mataimakin shugaban kasa kue dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP 2023, Alhaji Atiku Abubakar da kuma dan tsakarar shugaban kasa a jam iyyar Labour Mista Peter Obi ba za su iya tsayawa neman takara a babban zaben shekarar 2027 ba kasancewar sun zarta shekaru 60 da haihuwa a duniya.