Manchester United za ta gina sabon filin wasa mai cin ƴan kallo 100,000

Asalin hoton, X/Manchester United
Ƙungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sanar da aniyarta ta gina sabon katafaren filin wasa - wanda zai iya ɗaukar masu kallo kusan 100,000 - Mafi girma a Birtaniya.
Za a gina filin wasan ne kusa da filin wasanta na yanzu Old Trafford, kuma zai lakume kuɗi dala biliyan biyu da rabi.
United na ɗaya daga cikin sanannun ƙungiyoyin kwallon kafa a duniya, sai dai ta samu koma baya a baya-bayan nan da kuma rashin kataɓus.
Ƙungiyar na da bashin da ya kai dala biliyan 1.3 a kanta a halin yanzu.
Za a rushe filin wasa na yanzu, wato Old Trafford da zarar an kammala gina sabon.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka mallaki ƙungiyar, Sir Jim Ratcliffe ya ce yana son gina "filin wasa mafi ƙasaita a duniya", wanda ƙungiyar ke sa ran za a kammala a cikin shekara biyar.
Wannan sanarwa da ƙungiyar ta bayar na zuwa ne bayan doguwar muhawarar da ake kan ko za a yi wa filin na yanzu kwaskwarima ne ko kuma za a gina sabo.
Manchester United ta kasance tana amfani da Old Trafford ne tun shekarar 1910.
Ƙungiyar za ta ci gaba da wasa a filin na Old Trafford har sai an kammala gina sabon.

Asalin hoton, Manchester United











