An dakatar da Mbappe wasa ɗaya zai buga Copa del Rey da Barca

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kylian Mbappe zai buga wa Real Madrid wasan karshe a Copa del Rey da Barcelona a cikin watan nan, bayan da aka dakatar da shi wasa ɗaya.

An bai wa Mbappe jan kati ranar Lahadi, sakamakon ketar da ya yi wa Antonio Blanco a wasan da Real ta ci Alaves 1-0 a gasar La Liga.

A rahoton da alkalin wasan ya rubuta ya ce ya kori Mbappe ne, saboda ketar da ya yi, wanda hukuncin zai kama daga dakatarwa wasa ɗaya zuwa uku.

Da an dakatar da Mbappe wasa uku, kenan ba zai yi wa Real wasan karshe a Copa del Rey ba da Barcelona ranar 26 ga watan Afirilu.

An yi wa Mbappe sassaucin hukuncin, bayan da a rahoton alkalin wasan da ya rubuta ya ce ƙyaftin ɗin Faransa, ya yi kokarin taɓa ƙwallo ne.

Da wannan hukuncin, Mbappe ba zai buga wa Real Madrid wasan La Liga da Athletic Bilbao ba ranar Lahadi a Santiago Bernabeu ranar 20 ga watan Afirilu.

Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona mai jan ragama.

Mbappe ya ci ƙwallo 33 a wasa 49 a dukkkan karawa a Real a bana, tun bayan da ya koma ƙungiyar kan fara kakar nan daga Paris St Germain.

Ƙungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama za ta kara da Arsenal a Santiago Bernabeu a neman kai wa daf da karshe a Champions League ranar Laraba.

A makon jiya Arsenal ta doke Real Madrid 3-0 a zagayen kwata fainal a gasar zakarun Turai a Emirates.