Ya kamata Ingila ta gayyaci Maguire - Amorim

Asalin hoton, Getty Images
Ya kamata tawagar ƙwallon kafa ta Ingila ta gayyaci Harry Maguire in ji Ruben Amorim.
Maguire mai shekara 31, wanda ya buga wa Ingila wasa 64, yana daga cikin manyan ƴan wasan da kasar ba ta je da su gasar cin kofin nahiyar Turai EURO 2024 a Jamus ba.
Ingila ta kai karawar karshe, amma ta yi rashin nasara 2-1 a hannun tawagar Sifaniya a cikin watan Yulin 2024.
Maguire, wanda Erik ten Hag ya karɓe mukamin ƙyaftin daga wajensa a 2023, yana taka rawar gani a wasannin da Manchester United ke yi a kakar nan.
Shi ne ya ci Leicester City ƙwallo a FA Cup zagaye na huɗu da kuma zura ƙwallo a ragar Ipswich Town a Premier League a watan jiya.
Thomas Tuchel shi ne sabon kociyan tawagar Ingila, wanda ya maye gurbin Gareth Southgate.
Hukumar ƙwallon kafa ta Ingila ta nada tsohon kociyan Chelsea da Bayern Munich aiki, domin ya kai kasar gasar cin kofin duniya da za a yi a Amurka da Canada da Mexico a 2026.
Aikin farko da Tuchel zai fa ra shi ne jan ragama wasa biyu a Ingila, wadda za ta kara da Albania da kuma Latvia a wasan neman shiga gasar kofin duniya..
Tawagar Ingila ta taɓa lashe kofin duniya a 1966, lokacin da ta shirya wasannin.










