Ƙaruwar barazanar tuƙi cikin maye a titunan Nasarawa da Abuja

wasu motoci a kan hanya, inda aka ɗaura wa wata jarka uku , wani mutum ya juya bayansa a jikin wata mota

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Tuƙi cikin maye wani al'amari ne da kullum hukumomi ke gargaɗi kan aikata shi, saboda irin haɗarin da ke tattare da shi.

To sai dai da alama wanna matala na neman zama ruwan dare tsakanin direbobin bas da ke jigilar dimbin jama'a a jihar Nasarawa da ke arewa ta tsakiya Najeriya.

Lamarin a ya sa wasu ke ganin sakacin hukumomi wajen tabbatar da doka da oda a fannin sufin ƙasar.

Tuƙa abin hawa bayan direba ya sha maye, kasada ce ba ga rayuwarsa kaɗai ba, har ma da ta fasinjojin da ya ɗauka da kuma sauran mutanen da ke amfani da titi, da ma masu harkoki a gefen titin.

Wannan matsalar kan janyo asarar rayuka da dukiyoyi masu tarin yawa a Najeriya.

'Amfani da kayan maye ya zame min jiki'

...

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Wani direban motar bas da BBC ta zanta da shi a ɗaya daga cikin tasoshin motar da ke jigilar fasinja tsakanin Abuja da Keffi, ya ce saba da amfani da ƙwayoyi kafin tuƙi, kuma hakan ya zame masa jiki

"Idan har ban sha wata ƙwaya ba, bazan iya tuƙi cikin nutsuwa ba, ya riga ya zame min jiki'', in ji shi.

Ya ce dole sai ya sha maye sannan yake samun nustuwa.

''Idan ma ka ga na yi taɗi da fasinja, to sai na ga dama," in ji direban na bas da na ya nemi a sakaya sunansa.

Shi ma wani direban, ya ce kodayake shi ba ya shan maye kafin tuƙi, amma bai musanta wa wasu takwarorinsa direbobin ba.

"Ni ba na shan giya idan ina tuƙi. Idan ka sha giya ka hau sitiyari, ba kai ne ke tuƙi ba kenan, giyar ce ke tuƙi."

Ya kuma ba da misali da wani direba da ke yawan aiki ba tare da hutawa ba, saboda yana ganin yana da ƙwayar da zai sha.

"Na gaya masa ba daidai ba ne, sai ya ce ai shi ba shi da wata matsala tunda yana da ƙwayar da zai sha da ruwa, shikenan abin da yake buƙata."

A cewar direban ƙungiyarsu na ɗaukar matakai masu tsauri:

"Idan ƙungiyarmu ta kama wani direba ya sha giya ko wata ƙwaya ta maye kuma ya hau sitiyarin mota, zai rasa aikinsa ne'', in ji shi.

Me ƙungiyar direbobi ke cewa?

Ƙungiyar direbbin bas-bas na ƙaramar hukumar Karo ta ce tana ɗaukar matsalar da matuƙar muhimmanci.

Sakataren ƙungiyar, Mista Isuwa Maman, ya ce ƙungiyarsu ba ta yarda da shaye-shaye ba.

"Idan aka kama direba yana shaye-shaye, ana ƙwace masa lasisi, kuma ana kai shi ofishin ƴananda, direbobin da ke shaye-shaye ba direbobinmu ba ne. Muna da dokoki kuma muna sa ido akan su," in ji shi.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar ba ta wasa da lamarin shaye-shaye, kuma duk wanda aka kama yana shan giya ko ƙwaya zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Wane mataki FRSC ke ɗauka?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumar Kiyaye Aukuwar Hadurra ta Najeriya ta ce tana da matakai masu tsauri kan matsalar shan maye a lokacin tuƙi.

Mataimakin shugaban hukumar a jihar Nasarawa, Awwalu Magaji Muhammad, ya ce hukumar da na'urorin da za su iya gano direban da ya sha giya ko miyagun ƙwayoyi.

"Bayan an tabbatar direba yana cikin maye, ba za a bar shi ya ci gaba da tuƙi ba. Za mu ƙwace motarsa, za kuma mu yi masa tara sannan mu ba shi horo kan illar shaye-shaye'', in ji shi

Ya ci gaba da cewa hukumar ba za ta mayar masa da motarsa ba sai ya dawo hayyacinsa."

Ya ƙara da cewa idan direba ya ci gaba da shaye-shaye duk da matakan da ake ɗauka, to akwai matakin kotu.

"Za mu kai shi kotu domin a dakatar da shi gaba ɗaya daga tuƙi", in ji shi.

Matsalar shan giya da miyagun ƙwayoyi tsakanin direbobi ta jima tana ci wa al'umma tuwo a ƙwarya, kuma tana daga cikin manyan dalilan da ke haddasa haɗurra a titunan Najeriya.

Al'umma na ganin lokaci ya yi da hukumomi da jama'a za su tashi tsaye domin magance matsalar, wadda ke barazana ga rayuka, dukiya da kuma tsaron jama'a.