Zarge-zargen cin zarafin mata da Majalisar Dinkin Duniya ke watsi da su

An wallafa

Yadda Majalisar Dinkin Duniya ke tafiyar da harkokin kwarmata bayanai na bukatar bincike daga tawaga ta musamman daga waje, a cewar tsohuwar mai magana a madadin mata kan zargin lalata ko cin zarafinsu.

Kalaman Purna Sen na zuwa ne bayan da wani bincike na BBC ya bankado yadda aka raba ma'aikata mata da dama da aikinsu bayan sun yi kokarin bankado zarge-zargen aikata ba daidai ba a kansu.

Ms Sen ta ce MDD ta tashi tsaye ta kuma rungumi duk abubuwan da za su biyo bayan binciken.

MDD ta ce a shirya take wajen kare 'yancin masu kwarmata bayanai da tabbatar da cewa kowa na aikinsa yadda ya kamata.

Wani shirin BBC, mai taken Kwarmata bayanai: A zauren MDD, ya tattauna da ma'aikatan majalisar da suka yi kokarin bayar da rahoto kan wasu zarge-zarge - da suka hada da damfara da lalata.

Duk sun ce an hukuntasu bayan fitowa su bayar da bahasi - wasu ma an kore su daga aiki.

A shirin da aka naɗa, Ms Sen - mai magana a madadin mata kan cin zarafi ko tsangwama, da wariya a 2018 - ta ce akwai mata a MDD da ake zuwa mu su da "maganganun banza da fyade".

Idan kuma ana ci gaba da bari maza na cin karensu babu babbaka, a cewarta, "hakan zai ba su damar ci gaba da sheƙe ayarsu".

Ta fada wa shirin BBC na Newsnight cewa ba ta yi mamaki ba kan bayanan da suka biyo bayan bincike ko tattaunawa da irin wadannan mata.

"Tana mai cewa a galibinin lokuta, bai wa manyan ma'aikata kariya a cikin kungiya yafi muhimmanci kan karesu daga hadura daga mutanen da ke da karfin iko.

"Wannan na nufin akwai tsananin tashin hankali a cikin kungiyar wanda ya zarta batun kariya da ɗaga murya kan 'yanci ɗan dama, saboda wuri ne da galibi ake yiwa kallon cibiyar kare 'yanci.

"Amma har yanzu an gaggara tabbatar da bin wannan tsari a harkokin cikin gidanta ko masu yi mata aiki."

MS Sen ta ce tana son Sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres ta naɗa kwamiti na musamman na bincike domin tattara bayanan ma'aikata da mayar da hankali wajen daukan mataki.

A wata sanarwa, Ofishin Mista Guterres, ya ce kofa buɗe take kan duk wani batun na ciki da waje a kokarin shawo kan "munanan dabi'u ko rashin da'a".

Kariyar diflomasiyya

Majalisar Dinkin Duniya, na da kariya a shari'ance kuma manyan ma'aikatanta na sanye da rigar kariya ta diflomasiya daga duk dokokin kasa da kasa.

Wannan wani mataki ne na kare kungiyar daga ayyukanta ba tare da wani ya yi mata katsalanda ba.

Amma MDD na cewa ba wai ana bada wannan kariya ba ne, saboda bukatu na kai, don hakan wannan ba zai kare mutumin da ya aikata laifi ba, kamar cin zarafi ta hanyar lalata.

Dukkanin korafe-korafen ma'aikata dole a shawo kansu a cikin gida.

Ofishin da ke sa ido kan harkokin cikin gida na lura ko sa ido kan irin wadannan zarge-zarge masu girma, ciki har da manyan laifuka, sai dai ba shi da karfi na shari'a.

BBC ta samu wasu bayanan sirri da aka naɗa wanda ke nuna cewa Ofishin ba ya aiki yada ya dace.

An jiyo shugaban Ofishin, Ben Swanson, na magana a wani taron ma'aikata.

Yana cewa wata ma'aikaciya ta zo wajensa cikin hawaye da korafi, tana cewa akwai wani mataimakin sakatare janar da ya sa mata hannu a cikin wandonta.

Majalisar Dinkin Duniya (MDD), na da mataimaka da dama na sakatare Janar.

A muryar da aka naɗa, Mista Swason na cewa ya faɗawa sakatare janar da wasu manyan jami'an majalisar kan zargin cin zarafin - sai dai nan take aka tsayar da shi.

"Na yi kokari bada wannan labarin amma sai...aka katse ni." ana iya jiyo yana ambato hakan.

Ya kara da cewa an dakile matar daga fitowa ta fadi abin da aka aikata mata, an shaida cewa hakan ba zai mata amfani ba tun da mutumin da take da korafi a kansa "ɗan gaban goshi ne".

Peter Gallo - wanda ya kwarmata muryar da aka naɗa - ya shaidawa shirin BBC cewa: "Na shafe tsawon shekara hudu ina bincike a hedikwatar MDD da ke New York.

Kuma sakamakon abubuwan dana tattara, na tabbatar da cewa akwai rashawa sosai a kungiyar tun daga manyansu har kananan."

Bayan sauraron wadannan bayanai, Ms Sen na cewa: "Me ya sa sakatare janar bai ce komai ba, 'Wannan ya wuce tunani, yanzu me za mu yi a kai?

Tsari ne na aikin amincewa da irin wannan dabi'u na tunasar da ni daukan mataki," Sai kuma muka samu wasu bayanai da ke cewa "A'a kar mu kuskura mu doshi wajen."

Ofishin sakatare janar na MDD na cewa a tsaye ya ke wajen nuna jajircewa kan batun "ladabtar da kowanne ma'aikaci, kananan ko manya, da aka samu da hannu a cin zarafin lalata."

'Rashin ɗa'a'

Martina Bostrom, tsohuwar babbar mai ba da shawara a shirin MDD kan yaƙi da cutar HIV/AIDS, ta shaidawa BBC cewa ita ma ta fuskanci cin zarafi a wajen aiki. "Cin zarafi, amfani da mata da tsangwama na faruwa sosai a hedikwatar MDD, yana faruwa daga Litinin zuwa Juma'a.

Yana faruwa a lokutan ayyuka, yana faruwa a ko ina," a cewarta.

Ta ce jami'in majalisar Luiz Loures ne ya kai mata hari, mataimakin babban darakta a UNAIDS, kuma mataimakin sakatare janar, wanda ta ce ba shi da "da'a" kuma mutumin ne da aka san ba shi da tarbiyya.

A lokacin wani aiki da ya kai su Bangkok a 2015, ta ce ya yi amfani da karfi ya sumbaceta sannan ya rungumota a cikin lifta bayan barin wajen taro, kafin ya yi kokarin janta zuwa ɗakinsa.

"Na roke shi kan ya daina, ya bar ni na tafi. Sai na yi kokarin yi wa kai na katanga da kofar lifta saboda na tsaya a cikinsa.

"Ina cikin yanayi na fargaba sosai domin na tsorata lokacin da na hango wani zaure mai tsayi, a cewarta.

"Kwakwalwata ta rinka aiki cikin gaggawa, a hargitse nake, ban taba shiga wannan yanayi ba."

Martina ta shigar da korafi kuma ta yi magana da masu bincike na MDD da UNAIDS " sun mayar mun da martani cikin yanayi mai zafi da kaskanci," a cewarta.

"Yanayi ne mai ciwon gaske saboda ba shi da maraba da cin zarafina a kai a kai. Kamar ba sa ba wa mutum damar shakar numfashi."

A 2018, Luiz Lourez ya yi ritaya daga MDD kuma an gode masa na "shekaru 22 da ya kwashe yana aiki."

Ya shaida wa BBC cewa: "Ban taba cin zarafi ko aikata tsangwama kan kowanne mutum ba. Duk wadannan zarge-zarge ne marasa tushe."

MDD ta ce: "Zarge-zargen cin zarafi akan Dr Lourez ana bincike a kai," amma a wannan lokaci "ba ya cikin yanayin iya tsokaci kan wadannan zarge-zarge".

A Agustan 2021, Martina ta karbi wasika daga MDD, ta ke amincewa da batun "cin zarafinta na tsawon wani lokaci".

"Amma, kan batun cin zarafinta a 2015, sun ce abun ya faru ne da amincewarta don hakan bincikensu bai nuna ko bankado an yi mata amfani da karfi ba."

Surutan-baka

Ms Sen ta ce batun Martina wani bangare ne na irin tarin matsalolin da ke tattare da MDD.

Ta shaidawa shirin BBC cewa, galibi mata da dama ma'aikata sun fuskanci wani nau'i na salon cin zarafinsu a lokutan aiki, kuma galibi ba sa shigar da korafi.

"Abin da aka sani kan wannan batu bai taka kara ya karya ba, wannan batu ne mai muhimmanci, mutane na ganin kai rahoto zai bar baya da kura ko jefa su cikin tasku.

"Idan an kai mun irin wannan hari, ko zin zarafina. Zan so na kai kara. Amma ina iya jefa kai ni cikin hadari."

A wata sanarwa, Ofishin Sakatare Janar na MDD, Antonio Guterres, ya ce ana samun "cigaba da a yaki da matsalolin cin zarafi, wanda kusan a kowanne wajen aiki ba a rasawa".

Ya ce ana daukan matakai, irinsu daukan mata aikin bincike kan irin wadannan korafi, akwai layi na musamman da aka tanada domin ma'aikata suke shigar da korafi da horas da manyan ma'aikata.

Amma, a cewar shirin BBC na Newsnight, Ms Sen ya ce bayanan da aka tattara daga shirin ya nuna cewa MDD ba ta cika alkauranta na lamuntar wannan dabi'a ba kuma "da sauran aiki a gabansu".

"Ko batun zarge-zargen rashawa, damfara da lalata, (Ma'aikatan MDD) suna ganin basa samun cigaba ko da batun bayar da bahasi ne, ana watsi da korafinsu cikin gaggawa.

Ba kuma a bude musu kofa ko ba su damar daukaka ko kalubalantar kararsu," a cewarta.

"MDD ta shawo kan wasu bangarori da ta nuna gazawa a baya, amma dai ba a yi wani nisa ba.

Ina ganin abubuwan da suke kasancewa manyan matsaloli - da ke bukata kuma ana iya shawo kansu cikin gaggawa, ba wai surutan baka ba."