An ci PSG a gida a karon farko tun bayan Afirilun 2021

An wallafa

Paris St-Germain ta yi rashin nasara a gida a hannun Rennes a karon farko da aka doke ta a Ligue 1 tun bayan Afirilun 2021.

Ranar Lahadi Rennes ta ci PSG 2-0 a wasan mako na 28 a babbar gasar tamaula ta Faransa.

Wadanda suka ci mata kwallayen sune Karl Toko Ekambidaf daf da hutu, sannan Arnaud Kalimuendo ya kara na biyu a minti na uku da komawa zagaye na biyu.

Kenan Rennes ta yi wa PSG gida da waje kenan, bayan da ta fara yin nasara a kanta da cin 1-0 a gidanta ranar Lahadi 15 ga watan Janairun 2023.

An kuma kawo karshen wasa 35 da PSG ta yi a gida a filinta na Parc des Princes.

Itama Reims an kawo karshen wasa 19 da ta yi ba tare da rashin nasara ba, inda Marseille ta doke ta 2-1 ranar Lahadi.

Rabon da ta yi rashin nasara tun 3-0 a hannun Monaco a cikin watan Satumba.

Rennes - wadda ta ci PSG gida da waje a bana ta zama ta uku da ta yi hakan tun bayan da Qatar Sports Investments ya sayi Paris St Germain a 2011.

Rennes din tana mataki na biyar a teburin Ligue 1, biye da Monaco ta hudu.

Paris St Germain na nan a matakin farko a teburin Ligue 1 da maki 66, Marseile ce ta biyu mai maki 59.